Najeriya ta aike wa Jakadan Amurka sammaci kan furucin shugaba Trump
Ma’aikatar Kula da Harkokin Kasashen Waje jiya ta aika sammaci ga mataimakin shugaban ofishin jakadan Amurka da ke Abuja, David Young kan zargin furucin wariyar launin fata da ake zargin shugaba Trump ya yi inda ya bayyana ’yan Afirka da “kasashen wulakantattu”. An ruwaito cewa Mista Trump ya yi furucin ne makon da ya […]

Ma’aikatar Kula da Harkokin Kasashen Waje jiya ta aika sammaci ga mataimakin shugaban ofishin jakadan Amurka da ke Abuja, David Young kan zargin furucin wariyar launin fata da ake zargin shugaba Trump ya yi inda ya bayyana ’yan Afirka da “kasashen wulakantattu”.
An ruwaito cewa Mista Trump ya yi furucin ne makon da ya gabata yayin da ya halarci taro kan batun bakin haure.
Sai dai Trump ya musanta cewa shi ba mai ra’ayin nuna wariyar launin fata ba ne.
Trump ya yi musun ne yayin da yake tattaunawa da manema labaran fadar White Haouse a filin shakatawarsa da ke jihar Filorida a ranar Lahadin da ta gabata.