Najeriya ta ayyana Laraba da Alhamis ranakun hutun Babbar Sallah

Gwamnatin Najeriya ta ce ta bayar da hutun ne domin martaba miliyoyin musulman ƙasar.

Najeriya ta ayyana Laraba da Alhamis ranakun hutun Babbar Sallah

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Laraba, 27 ga watan Mayu da Alhamis, 28 ga watan a matsayin ranakun hutu a fadin Najeriya domin shagulgulan Babbar Sallah.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da babbar sakatariya a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dokta Magdalene Ajani ta fitar a yammacin ranar Litinin.

Sanarwar wadda aka fitar a madadin Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ta ce gwamnati ta bayar da hutun ne domin martaba miliyoyin musulman ƙasar.

Sanarwar ta ce an bayar da hutun ne domin musulman ƙasar su samu damar gudanar da shagulgular Babbar Sallah kamar yadda sauran Musulman duniya ke gudanarwa.

Ministan ya kuma taya al’ummar musulman na ciki da wajen ƙasar murna, tare da kiran su yi amfani da wannan muhimmin lokacin domin yi wa ƙasar addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaba.

A ranar Laraba ne musulman duniya za su gudanar da Idin Babbar Sallah bayan tsayuwar Arfa da mahajjata za su yi a Saudiyya ranar Talata.