Najeriya ta ci lambobi 18 a gasar Kareti a kasar Mali
Najeriya ta samu lambobi 18 a gasar Kareti na farko na kasashen Afirka ta Yamma da aka kammala a kasar Mali. Shugaban Hukumar Wasan Kareti ta Kasa, Mista Silas Ali Agara ya shaida wa Aminiya cewa, “Najeriya ta tabuka a wasan Kareti na farko da aka gudanar a birnin Bamako na kasar Mali.” Ya ce, […]
Najeriya ta samu lambobi 18 a gasar Kareti na farko na kasashen Afirka ta Yamma da aka kammala a kasar Mali.
Shugaban Hukumar Wasan Kareti ta Kasa, Mista Silas Ali Agara ya shaida wa Aminiya cewa, “Najeriya ta tabuka a wasan Kareti na farko da aka gudanar a birnin Bamako na kasar Mali.”
Ya ce, kasar Senegal ce ta zo ta farko inda ta kwashe lambobi 27 da suka hada da gwal 19 da azurfa 2 da tagulla 6; kasar Burkina Faso ta yi ta biyu da lambobi 13 da suka hada da gwal 5 da azurfa 5 da tagulla 3, sai kasar Mali ta zo ta uku da lambobi 28 da suka da gwal 4, azurfa 7 da kuma tagulla 17.
Mista Silas Ali Agara ya kara da cewa, Najeriya ta zo ta hudu da lambobi 18 da suka hada da gwal 2 da azurfa 9 da kuma azurfa 7.
Sauran kasashen da suka halarci gasar sun hada da Benin da Guinea da Cote D’iboire da suka zo na biyar da na shida da bakwai a jere.
Ya ce sauran kasashen da suka halarci gasar amma ba su ci ko lamba daya ba su ne: Gambiya da Togo da Saliyo da Ghana da Nijar da Cape Berde da Liberiya da kuma Guinea Bissau.
Mista Silas Ali Agara ya ce, wasan Kareti ya fara habaka a Najeriya domin ga shi har an samu lambobin yabo, duk da cewa wasan Karetin ya fi bunkasa a kasashen da suka fi Najeriya a gasar.