Najeriya ta cika shekara daya babu bullar cutar poliyo
Najeriya ta kama hanyar yin ban kwana da cutar poliyo (shan inna) bayan da ta cika shekara guda cur ba a samu bullar cutar ba a daukacin kasar nan a ranar Juma’ar da ta gabata. Wata sanarwa da ta fito daga Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA), ta bayyana haka inda ta ce […]
Najeriya ta kama hanyar yin ban kwana da cutar poliyo (shan inna) bayan da ta cika shekara guda cur ba a samu bullar cutar ba a daukacin kasar nan a ranar Juma’ar da ta gabata.
Wata sanarwa da ta fito daga Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA), ta bayyana haka inda ta ce rabon da a samu bullar cutar poliyo a kasar nan shekara guda ke nan, tun lokacin da aka samu wani yaro mai wata 16 ya kamu da cutar a karamar Hukumar Sumaila da ke Jihar Kano.
Sanarwar ta ce, idan duk gwaje-gwajen da aka gudanar suka nun aba a samu bullar cutar a sauran sassan kasar nan ba nan da ’yan makonni, za a cire sunan Najeriya daga cikin kasashen da suke fama da annobar poliyo.
Sai dai kuma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ba za ta bayyana Najeriya ta yi ban kwana da cutar poliyo ba, sai ta kai shekarar 2017 ba tare da an sake samun bullar cutar a fadin kasar nan ba, sannan ta kara sanya ido tare da inganta gudanar da allurer rigakafin cutar.
Zuwa shekarar 2012 an samu bullar cutar poliyo 122 a sassan kasar nan, bullar cutar mafi yawa a duniya. Wannan ya sa Minista a Ma’aikatar Lafiya da ya bar gado Injiniya Fidelis Nwankwo, ya ce, “Idanunwanmu suna bude, kuma wannan ne lokaci mafi muhimmanci na wannan shiri. Saboda idon duniya yana kanmu wajen magance cutar, don haka babu batun sakaci har sai mun cimma nasarar kawar da wannan cuta nan da shekarar 2017.”
Babban Daraktan Hukumar NPHCDA Dokta Ado Muhammad ya ce: “Yanzu muna duba yiwuwar kawar da cutar nan da shekarar 2017. Mun sadaukar da kai wajen nemo ingantattu hanyoyin kawar da duk matsalolin da suke kawo mana tarnaki har sai mun cimma nasarar kawar da cutar a kasar nan. Mun lura akwai bukatar a kara zage damtse tare da kara himma domin tabbatar da mun kai ga kowane yaro.”
Sanarwar ta yaba wa dukkan wadanda suka taka rawa wajen gudanar da allurer rigakafi da sarakuna da shugabannin addini da iyaye da masu kula da ’ya’ya da dukkan wadanda suka taimaka wajen yaki da cutar poliyo a kasar nan duk da irin kalubalen da aka rika samu.
“Yau rana ce ta tarihi a fannin kiwon lafiya ga ’yan Najeriya. Kuma a yanzu muna kira ga daukacin ’yan Najeriya – jami’an kiwon lafiya da sarakuna da shugabannin addini da na siyasa da na al’umma da su kansu al’ummar su taimaka mana wajen tsare wannan nasara don ganin an kawar da poliyo nan da shekarar 2017, lokacin da Hukumar WHO za ta ayyana Najeriya cewa ta yi ban kwana da poliyo. Kada mu yi kasa a gwiwa har sai mun hada hannu don cimma wannan manufa don amfanin kasarmu, aiki ya fi dacewa,” inji Dokta Ado Muhammad.