Najeriya ta ciri tutar yaki da cutar shan inna

A wani labari mai sosa rai daga Hukumar Kiwon lafiya Matakin farko ta Tarayya, wanda aka watsa ta kafar sadarwar yanar gizo, ranar 24 ga watan Yulin 2015, na cewa Najeriya na dab da ban kwana da cutar shan inna. Babban Darektan wannan hukumar, Dakta Ado Mohammed, wanda shi da kansa ya yi wannan furuci, […]

Najeriya ta ciri tutar yaki da cutar shan inna
Najeriya ta ciri tutar yaki da cutar shan inna

A wani labari mai sosa rai daga Hukumar Kiwon lafiya Matakin farko ta Tarayya, wanda aka watsa ta kafar sadarwar yanar gizo, ranar 24 ga watan Yulin 2015, na cewa Najeriya na dab da ban kwana da cutar shan inna.
Babban Darektan wannan hukumar, Dakta Ado Mohammed, wanda shi da kansa ya yi wannan furuci, cewa: “Idan sakamakon gwaje-gwaje da ake yi ya bayyana babu wata cuta mai kama da shan inna, to lallai za a a iya sanya kasar nan a matsayin ta tsarkake kanta daga cutar shan inna.Yau kusan shekara guda ke nan mutum na baya-bayan nan, yaro dan wata shida a cikin karamar Hukumar Sumaila ta Jihar Kano aka samu dauke da kwayar cutar shan inna.
Sanarwar ta kara da cewa za a aiyana Najeriya a matsayin kasar da babu mai dauke da cutar shan inna a shekara 2017.  Idan har kasar ta matsa kaimi na dorewa kan matakan da ta dauka na yaki da cutar, ta hanyar inganta yin allurar riga-kafin shan inna, za a cimma nasarar da ke nuni da cewa babu wanda ke dauke da cutar cikin shekara daya. Wannan kuwa matakin farko ne wajen samun lambar amincewar kawar da cutar dungurungum a kasar kafin shekara 2017.
Rigakafin a kan kari zai taimaka gaya wajen shawo kan sauran matsaloli da kan zame kafar ungulu wajen yakar cutar shan inna, da kuma diga wa yara sinadarin kariya a jikinsu. Wannan na nuni da cewa Najeriya ta cirri tuta wkajen yaki da cutar shan inna.
Har ila yau, zai ba da damar sanin in akwai wani da ke boye da cutar. Idan kuma muka dubi wannan nasara da hukumar samar da lafiya matakin farko a Jihar Adamawa ta samu, za mu ga cewa ta taka rawar gani idan aka yi la’akari da fadakarwar da take yi a kan kari game da yaki da cutar da muhimmancin rigakafin ga yara. Wannan hukuma ta fadada, tare da inganta sa-ido kan cutar,  kuma an kara inganta shirin rigakafi, domin ta shiga kowane lungu da sako na jihar, har da yankunan da ke Arewacin Jihar Adamawa, inda ’yan kungiyar Boko Haram suka lalata garuruwa da kauyuka.
Hukumar samar da kiwon lafiya matakin farko na kaffa-kaffa da aikinta da ta kai ga samun nasarar allurar rigakafi a yankunan da taimakon jami’an tsaro kamar sojoji da ‘yan sanda da  jami’an shige da fice da kuma ‘yan banga. Ganin muhimmancin da rawa da kafofin yada labarai ke takawa wajen isar da sako ga dimbin jama’a  cikin kankanin lokaci ya sanya hukumar a nan Jihar Adamawa ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen amfani da kafofin yada labarai da ke jihar, kamar gidajen rediyon da suka hada da na jiha (ABC Yola) da na gwamnatin tarayya (FRCN, FOMBINA F.MYola) da gidan rediyo da Talabijin masu zamankansu (TbGotel da RediyoGotel) da gidajen talabijin na jiha (ATbYola) da na gwamnatin tarayya (NTA Yola) da kuma jarida mallakar jiha (The Scope), don fadakar da iyaye kan muhimmancin yi wa yaransu allurar rigakafi da ranakun yin allurar bai cin bitoci da take shirya wa iyaye kan hanyoyin kariyar mace- macen yara da mata masu juna biyu lokacin haihuwa.
A Jihar Adamawa don ganin an samu kawar da cutar shan inna lokacin rigakafin.  Ana ganin ma’aikatan kiwon lafiya na fitowa daga sakatariyar kowace karamar hukuma dauke da kayyakin aiki daban-daban, suna nausawa lungu da sako, amma a wasu lokuta sukan tafi da jami’an tsaro don kauce wa bacin rana wajen kai musu hari.
Bello Hamman gode, babban sakataren hukumar samar da kiwon lafiya matakin farko na karamar Hukumar Yola ta Arewa, kafin ranar 24 ga watan Yulin shekara 2015 yana kaiwa da komowa, ya hada zufa sabili da aikin rarraba allurar rigafi da sauran kayayyaki da suka wajaba na rigakafi ga ma’aikatan kiwon lafiya da za su gudanar da aiki a yanki.
A  lokacin da nake rubuta wannan makala akasarin manyan sakatarorin hukumar samar da kiwon lafiya matakin farko da ke Jihar Adamawa,  musamman wadanda ’yan tada kayar baya suka shafa da suka hada da kananan hukumomin Michika da Madagali da Mubi ta Arewa da Mubi  Kudu da Maiha da Gombi da Song na aiki babu kama hannun yaro don tabbatar da an samu nasarar gudanar da allurer rigakafi a yankunansu.
Sun sanya shugabanin gargajiya da suka hada da Hakimai da Dagatai da masu unguwanni wajen fadakar da jama’amuhimmancin rigakafi, tare da dakile duk wata kafa da kan iya zamewa tarnaki wajen samun nasarar yin allurar rigakafi.
Dole ne kuma a jinjina wa hukumar samar da kiwon lafiya matakin farko da ke Jihar Adamawa, sabili da namijin kokari da ta yi na kai dauki ga ‘yan gudun hijira da ke samun mafaka a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Jimeta da Yola da suka hada da Bajabure da Malkohi da Kwananwaya da Damaturu.
Hukumar samar da kiwon lafiya matakin farko ta cigaba da gangamin wayar wa jama’a kai game yadda za su kare kansu daga daukar kowane nau’in cuta kamar ciwon huhu da zawo  da kyanda.  Ana fadakar da mata masu juna biyu kan muhimmancin ziyartar asibiti da wasu cibiyoyin kiwon lafiya, don samun kauce wadaga yin bari ko samun matsala yayin haihuwa.
Hukumar ta samu cimma wadannan nasarori ne sabili da shugaban cinagari da shugaban hukumar Dokta Abdullahi Dauda Belel ke yi, Za ka iske Dokta Abdullahi Dauda Belel kowane lokaci a ofisoshi in tafiyar zuwa aiki walau a Abuja ganin shi memba ne na hukumar kula da kiwon lafiya matakinfarko ta tarayya ko kuma zuwa wata aiki a kasar waje.
Wannan shugaba ya sa mu goyon bayan wadannan mukarrabansa
Emmanuel Kwache,  dan Jarida mai zaman kansa, kuma mai sharhi kan lamuran yau da kullum.  Ya rubuto daga No.1 Titin Abaji Sabon Hanya Anguwan Kabawa   Yola, imail: [email protected] 08059116547, 08087721702.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50