Najeriya ta fita daga matsin tattalin arziki

Wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Kasa ta fitar ya nuna Najeriya ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta shiga.   Rahoton wanda Hukumar NBS ta fitar a yau Talata ya nuna cewa kasar ta fita daga cikin matsin tattalin arzikin bayan da tattalin arzikin kasar ya rika karuwa mataki-mataki.   Shugaban Hukumar Kididdigar […]

Najeriya ta fita daga matsin tattalin arziki

Wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Kasa ta fitar ya nuna Najeriya ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta shiga.
 
Rahoton wanda Hukumar NBS ta fitar a yau Talata ya nuna cewa kasar ta fita daga cikin matsin tattalin arzikin bayan da tattalin arzikin kasar ya rika karuwa mataki-mataki.
 
Shugaban Hukumar Kididdigar na Kasa, Dokta Yemi Kale ne yabayyana wa cibiyar bincike ta Bloomberg a kwanannan cewa kasar za ta iya fita daga matsin tattalin arzikin da ta shiga a watannin ukun masu zuwa.
 
“Za mu iya fita daga matsin tattalin arziki a watanni uku masu zuwa. Idan kuwa hakan ta auku to babu shakka zai rage kalubalen da tattalin arzikin ke fuskanta”. Inji shi