Najeriya ta gindaya wa makwabtanta sharuddan kan sake bude iyakokinta

Gwamnatin Tarayya ta gindaya sharuddan da tilas sai kasashen da ke makwabtaka da Najeriya sun cika kafin ta sake bude kan iyakokinta. A ranar Litinin ce Ministan Harkokin Kasashen Waje, Mista Geoffrey Onyeama ya bayyana haka bayan tashi daga taron da kwamitin lura da rufe kan iyakokin Najeriya na wucin-gadi ya yi. Wani rahoto ya […]

Najeriya ta gindaya wa makwabtanta sharuddan kan sake bude iyakokinta

Daga hagu Jarumin Nollywood, Jide Kosoko, sai Sakatariyar Gwamnatin Jihar Legas Misis Folashade Jaji da Mataimakiyar Darakta ta Hukumar Kula da Harkokin Caca da gasannin cin kuxi ta Najeriya, Shiyyar Legas Misis Joy Okuna a wajen miqa kyaututtuka na farko na gasar sanya kati ka kashi garavasa na Kamfanin Glo mai taken (My Own Don Beta) da aka gudanar a unguwar Ojuelegba da ke Legas ranar Larabar makon jiya.

Gwamnatin Tarayya ta gindaya sharuddan da tilas sai kasashen da ke makwabtaka da Najeriya sun cika kafin ta sake bude kan iyakokinta.

A ranar Litinin ce Ministan Harkokin Kasashen Waje, Mista Geoffrey Onyeama ya bayyana haka bayan tashi daga taron da kwamitin lura da rufe kan iyakokin Najeriya na wucin-gadi ya yi.

Wani rahoto ya rawaito cewa wasu sharudda da ka’idoji da Ministan ya bayyana kafin sake bude kan iyakar sun hada da cewa: Duk wani kayan da za a shigar daga wata kasa da ke karkashin Kungiyar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma (ECOWAS), su zamo ba afarke kwalayen su ba.

Kuma kayan su kasance jami’an waccan kasar sun rako su har bakin iyakar Najeriya, su damka kayan ga jami’an Kwastam na Najeriya kamar yadda kayan suka fito daga kasashen da aka sayo su, ba tare da an farke kwalayensu ko an yi musu mazubi ba.

Ya ce Najeriya ba za ta amince da yin kumbiya-kumbiya a wannan tsari ba.Sauran sun hada da cewa kayan da ake yi a kasashen Kungiyar ECOWAS su kasance ingancinsu ya kai sharuddan da ECOWAS ta gindaya.

Sannan kuma kayayyakin da za a rika shigowa da su daga kan iyakokin Najeriya, su kasance kayayyaki ne da ake sarrafawa a cikin wadancan kasashe. Kuma kayan da za a shigo da su daga wasu kasashen da ba na ECOWAS ba, sun kasance ingancinsu ya haura sharuddan na ECOWAS da kashi 30 cikin 100. Saboda kasashen ECOWAS tilas su karfafa cinikayya a tsakaninsu.

Sauran sun hada da dole sai an rushe dukkan wasu manya da kananan rumbunan ajiyar kayayyaki da ke kan iyakokin kasashen da suka yi makwabtaka da Najeriya. Sannan tilas a rika daure kayan da za a shigo da shi a cikin kwalaye ko buhuna masu ingancin saboda ba kowane irin tarkace ne Najeriya za ta sake bari a shigo ma ta da shi daga wasu kasashe ba.

Duk dan wata kasar da zai shigo Najeriya ko wani wanda zai fita daga Najeriya, tilas ya kasance ya fita ko ya shigo kan iyakokin da aka amince a shigo. Kuma ya kasance ya kai kan sa wurin jami’an kula da shigi da fice da ke kan iyakar, kuma ya kasance ya na da takardun amincewa shigowa kasar nan.

Nan da makonni biyu Najeriya za ta dauki nauyin zaman nazarin wannan ka’idoji tare da wakilai daga Jamhuriyar Benin da Nijar da na Najeriya.

Shugabannin Ma’aikatun Harkokin Waje da Cikin Gida da Kudade da Kwastam da Shige-da-fice da tsaro na NIA da sauran jami’an bangarorin tsaro na kowace kasashen uku za su kasance cikin wannan kwamiti.

Shugaba Muhammadu Buhari dai ya ce sai ranar 31 Ga Janairu, 2020 sannan za a sake jaraba bude kan niyakokin.