Najeriya ta kai matakin kusa da na ƙarshe a Gasar AFCON

Najeriya ta yi wa Angola ci ɗaya mai ban haushi.

Najeriya ta kai matakin kusa da na ƙarshe a Gasar AFCON

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta doke Angola a wasan kwata-final da suka fafata a Gasar Kofin Nahiyyar Afirka ta AFCON.

Tun kafin tafiya hutun rabin lokaci Najeriya ta yi wa Angola ci ɗaya mai ban haushi wadda ita ce ta raba gardama har aka karkare wasan.

Da wannan sakamakon dai yanzu Super Eagles ta kai matakin kusa da na ƙarshe a gasar da ake ci gaba da kece raini a Kasar Ivory Coast.

Dan wasan gaban Najeriya, Ademola Lookman ne ya samu damar zura kwallon daya tilo a ragar Angola a minti na 41 da fara wasan.

Yanzu da wannan nasarar Super Eagles ita ce kasa ta farko da ta samu tikitin kai wasan na kusa da na karshe.

Najeriyar za ta fafata da Afirka ta Kudu ko Caper Verde da za su buga wasan dab da na kusa da na karshe ranar Asabar.