Najeriya ta karbi rigakafin COVID-19 daga Rasha
Gwamnatin Najeriya ta karbi samfarin rigakafin allurar rigakafin cutar coronavirus daga kasar Rasha. Kafar watsa labarai ta Channels ta rawaito cewa Ambasadan Rasha a Najeriya, Alexey Shebarshin shi ya mika samfurin ga Ministan Lafiya Dokta Osagie Ehanire, a lokacin da ya kai ziyara ma’aikatar ranar Juma’a a Abuja. Ambasadan ya kuma mika taimakon wasu kundin […]
Gwamnatin Najeriya ta karbi samfarin rigakafin allurar rigakafin cutar coronavirus daga kasar Rasha.
Kafar watsa labarai ta Channels ta rawaito cewa Ambasadan Rasha a Najeriya, Alexey Shebarshin shi ya mika samfurin ga Ministan Lafiya Dokta Osagie Ehanire, a lokacin da ya kai ziyara ma’aikatar ranar Juma’a a Abuja.
Ambasadan ya kuma mika taimakon wasu kundin bayanai da za su taimaka wa Najeriya a kan rigakafin na COVID-19 ta yadda za ta fadada bincike.
“Mun dukufa wajen tattara bayanan ilimi domin samar da kayan aikin da su taimaka wajen jinya da kuma samar da alluran rigakafi.
“Mun bayyana sha’awarmu a kan rigakafin cutar COVID-19 don mu samu damar fadada bincike ta yadda za mu yi aiki kafada da fafada”, inji ministan.
- Soja ya bindige karamin yaro a Fadar Shehun Borno
- Likitoci za su tsunduma yajin aiki
- An kashe matashi a rikicin teburin mai shayi
Ya ce, Najeriya ta kasance daya daga cikin kasashe da suke fadada musayar binciken ilimi da hukumomi da kuma kasashe da dama domin dakile yaduwar cutar.
Ehanire ya yaba wa Ofishin Jakadancin Rasha a Najeriya bisa yadda ya bawa Najeriya damar mallakar samfurin rigakafin, lokaci kadan bayan Gwamnatin Rasha ta fitar da bayanin samar da ragakafin