Najeriya ta karbo bashin kudi a mulkin APC sama da na PDP- Dino Melaye
Shugaban Kwamitin Babban Birnin Tarayya Abuja na Majalisar Dattawa, Sanata Dino Melaye ya ce an karbo bashin kudi kimanin Naira triliyan 11 a shekara uku kawai a mulkin APC, sama da na PDP da suka karbo bashin Naira triliyan 6 a shekara 16 da suka yi suna mulki. Melaye ya yi wannan jawabin ne a […]
Shugaban Kwamitin Babban Birnin Tarayya Abuja na Majalisar Dattawa, Sanata Dino Melaye ya ce an karbo bashin kudi kimanin Naira triliyan 11 a shekara uku kawai a mulkin APC, sama da na PDP da suka karbo bashin Naira triliyan 6 a shekara 16 da suka yi suna mulki.
Melaye ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake nuna rashin jin dadinsa da yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da kudurin kafa Peace Corps, inda ya ce ba ta da wani takaimaiman shiri na tallafa wa matasa.
“Lokacin da za a kafa rundunar civil defence haka aka ce babu kudi, amma gashi yanzu ana cin moriyarsu ta yadda suke taimakawa wajen bayar da tsaro.”