Najeriya ta kashe kusan Naira tiriliyan 2 wajen shigo da dabbobi da fatunsu
Najeriya ta kashe kimanin Naira tiriliyan 1 da biliyan 650 wajen shigo da dabbobi da fatu a cikin shekara hudu duk da cewa kasar nan na da damar sarrafa nata na cikin gida. Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta ce a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2017 Najeriya ta kashe Naira tiriliyan 1 da biliyan 320 […]
Najeriya ta kashe kimanin Naira tiriliyan 1 da biliyan 650 wajen shigo da dabbobi da fatu a cikin shekara hudu duk da cewa kasar nan na da damar sarrafa nata na cikin gida.
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta ce a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2017 Najeriya ta kashe Naira tiriliyan 1 da biliyan 320 wajen shigo da dabbobi masu rai cikin kasar nan. A bisa nazarin da Aminiya ta yi, ta gano cewa safarar shigo da dabbobi masu rai din kadai, ya kai kimanin kashi 16.52 na adadin dukan kayayyakin da Najeriya ke shigowa da su daga kasashen ketare a cikin shekara hudun da suka gabata.
kididdigar ta ce a tsakanin shekarun 2014 zuwa 2017, Najeriya ta shigo da kayayyakin da suka kai Naira tiriliyan 32 da biliyan 450 wanda ya yi kasa da kimanin Naira tiriliyan 48.2 wajen shigo da kayayyakin a cikin zango guda. Wannan kuma lamari ne da ke nuni da hauhawar shigo da kayayyakin waje sannan da saukar fitar da kayayyakin kasar nan zuwa ketare.
Har ila yau kididdigar ta ce Najeriya na shigo da kayayyakin da suka shafi dabbobi da fatun dabbobin tudu da na ruwa da man dafa abinci na kimanin Naira biliyan 321 da miliyan 55 a duk shekara. Wannan na nuna cewa Najeriya ba ta tabuka abin a zo a gani game da fitar da dabbobi da fatu da man dafuwa idan aka kwatanta da adadin wadda take shigowa da su.
Daga shekarar 2014 zuwa 2017 Najeriya ta fitar da dabbobi masu rai da fatu na kimanin Naira biliyan 69 da miliyan 670, adadin da bai kai kashi 10 na adadin wadanda ta shigo da su a wancan lokaci ba. Wannan kididdiga ta ja hankalin masana ganin yadda Najeriya ke tafka asara a rububin shigo da fatu da takalma da jakunkunan da take yi, maimakon yin amfani da wannan damar wajen sarrafa su a kamfanoninmu na cikin gida da ke Legas da Kano da Aba.
A kwanakin baya Gwamnatin Tarayya ta ce tana kashe fiye da Naira biliyan 468 wajen shigo da madara da yagot kadai a shekara.
A yayin da take bayani a lokacin kaddamar da wani kwamiti na musamman da zai duba yiwuwar farfado da sarrafa kayayyakin cikin gida maimakon shigo da kwatankwacinsu daga kasashen waje a Abuja, Minista a Ma’aikatar Masana’antu da Kasuwanci, Hajiya A’isha Abubakar ta ce Najeriya tana da dukan damar inganta kayayyakinta na cikin gida wanda zai samar da miliyoyin ayyukan yi sannan da tara kudin harajin da zai kai akalla Naira biliyan 300 a duk wata.
Ministar wacce Babban Sakataren Ma’aikatar Mista Edet Sunday Akpan, ya wakilta a wajen taron, ta ce kididdiga ta nuna cewa Najeriya tana da dabbobi kimanin miliyan 19 da dubu 500, wadanda fiye da kashi 80 mallakar daidaiku n mutane ne da suka hada da Fulani makiyaya da kananan gidajen gona, yayin da sauran ke karkashin manyan manoma da kamfanoni.