Najeriya ta ki amsar danta mai neman mafaka a Ingila

Dan Najeriyar nan Isa Mu’azu ya koma Birtaniya bayan da hukumomin Najeriya suka tilasta wa jirgin da yake ciki juyawa daga kasar nan.Lauyoyin Isa Mu’azu wanda yake yajin cin abinci har tsawon kwanaki 100, sun ce ya koma zuwa cibiyar da ake tsare da shi ta Harmondsworth a Birtaniya. Ana tunanin cewa hukumomin Najeriya ba […]

Najeriya ta ki amsar danta mai neman mafaka a Ingila

Dan Najeriyar nan Isa Mu’azu ya koma Birtaniya bayan da hukumomin Najeriya suka tilasta wa jirgin da yake ciki juyawa daga kasar nan.
Lauyoyin Isa Mu’azu wanda yake yajin cin abinci har tsawon kwanaki 100, sun ce ya koma zuwa cibiyar da ake tsare da shi ta Harmondsworth a Birtaniya. Ana tunanin cewa hukumomin Najeriya ba su ba jirgin da ya dauko shi iznin sauka ba ne, amma hukumomin Najeriya sun musunta hakan.
Malam Mu’azu ya nemi mafaka a Burtaniya ne bisa hujjar cewa masu tsaurin ra’ayin addinin Musulunci a Najeriya za su kashe shi.
Sai dai ma’aikatar cikin gida ta Birtaniya ta yi watsi da dalilansa, sannan ta yi yunkurin tusa keyar Mu’azu mai shekara 45 zuwa gida a ranar Juma’ar da ta gabata. Jirgin da ke dauke da Mu’azu wanda aka yi shatarsa ya shafe sa’o’i da dama a sararin samaniyar Najeriya, amma ba a ba shi iznin sauka ba. Ana tunanin jirgin ya tsaya a kasar Malta na sa’o’i biyu kafin ya koma Birtaniya.
‘Yajin cin abinci’
Lauyoyinsa sun ce Mu’azu ya koma bangaren kula da marasa lafiya a wurin tsaro na Harmondsworth.
Ma’aikatar cikin gidan Birtaniya ta ki cewa komai a kan abin da ya faru, amma an fahimci cewa jami’anta na aiki tare da gwamnatin Najeriya domin mayar da shi gida.
Isa Mu’azu wanda dan asalin Jihar Bauchi ne ya kasance a tsare tun lokacin da ya yi ikirarin neman mafaka a watan Yulin da ya gabata, inda ya ce wai yana fuskantar barazana daga kungiyar Boko Haram
Ya shiga Birtaniya ne a matsayin bako a watan Yulin shekarar 2007, kuma ya zauna ba tare da izini ba bayan da takardar iznin zamansa ta kare a watan Janairun shekarar 2008.
Sai dai kuma hukumomin sufurin jiragen sama na Najeriya sun musanta rahotannin da kafofin watsa labarai na Birtaniya suka bayar cewa sun hana jirgin da ke dauke da Isa Mu’azu sauka a Najeriyar.
Kakakin Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya Mista Yakubu Dati ya ce, Najeriya ba ta hana jirgin sauka ba.
Ya ce abin da ya faru shi ne hukumomin ba su kammala shirye-shiryen da suka kamata ba, saboda haka ne matukin jirgin ya sauka a Malta domin jira a kammala shirya-shiryen.
Ya ce gwamnatin Najeriya ta ba da dukkanin dama kuma da zarar jami’an Birtaniya sun kammala shirye- shirye jirgin zai kamo hanya zuwa Najeriya