Najeriya ta koma amfani da tsohon taken kasarta

An sauya taken Najeriya daga ‘A rise O compatriots’ zuwa ‘Nigeria we hail thee.’

Najeriya ta koma amfani da tsohon taken kasarta
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar komawa amfani da tsohon taken Najeriya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar cewa shugaban kasar ya sanya hannu kan dokar a ranar Laraba.

A ranar ce Shugaban Tinubu kai ziyara zauren majalisar inda ya jagoranci sake kaddamar da tsohon taken Najeriyan da aka dawo da shi.

A bisa sabuwar dokar, taken Najeriya da ya fara da ‘Nigeria we hail thee,’ zai ci gaba aiki; shi kuma , ‘A rise O compatriots’ zai koma masayin addu’ar kasa.

Shugaban kasar ya bukaci majalisar ta hada kai da bangaren zartarwa domin amfanin al’ummar kasar.

Da yake wa al’ummar kasar murnar cika shekaru 25 a karkashin mulkin dimokuradiyya babu yankewa, shugaban kasar ya yi kira al’ummar kasar kada su kawo nakasu ga tsari.

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS

Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar rushe Hukumar EFCC

HOTUNA: Jana’izar tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa Lagbaja