Najeriya ta kulla yarjejeniyar iskar gas da kasar Equatorial Guinea

Tinubu da shugaban Equatorial Guinea sun sanya hannu kan yarjejeniyar

Najeriya ta kulla yarjejeniyar iskar gas da kasar Equatorial Guinea

Shugaba Tinubu da takwaransa na ƙasar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar bututun iskar gas tsakanin kasashen biyu.

Shugabannin sun sanya hannu ne daren Laraba inda Tinubu ya bayyana a matsayin babban ci gaba a fannin albarkatun iskar gas a nahiyar Afirka.