Najeriya ta maida wa Nijar wutar lantarki
Najeriya ta amince ta dawo da wutar lantarki da ta yanke wa Nijar bayan kungiyar ECOWAS ta dage takunkumin da ta sanya wa Nijar da kawayenta
Najeriya ta amince ta maido da wutar lantarki da ta yanke wa Jamhuriyar Nijar bayan kungiyar ECOWAS ta dage takunkumin da ta kakabawa kasashen Nijar din da Mali da Burkina Faso kuma Guinea.
ECOWAS ta dage takunkumin ne bayan babban taron kungiyar kan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro da ya gudana a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja.
Shugaban Najeriya kuma shugaban ECOWAS, Bola Tinubu, ya ce, saboda haka “Najeriya sa ta dawo da wutar lantarki da ta yanke wa Nijar ba tare da bata lokaci ba.”
A watan Agustan bara ne Najeriya ta katse wutar lantarki da take ba wa Nijar a matsayin wani bangare na takunkumin da ECOWAS ta kakaba saboda juyin mulkin da sojojin Nijar suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum.
- Boko Haram Ta Sake Lalata Turakun Wutar Lantarki Mai Karfin 330KVA A Yobe
- EFCC ta tsare masu sayar da sabbin takardun kudi a Kano
Al’ummar Nijar, musamman mazauna manyan birane sun shiga damuwa saboda rashin wutar lantarkin.
A watan Nuwamba ne dai sanatoci daga Arewacin Najeriya suka bukaci Tinubu ya mayar wa Nijar wutar.
A ranar Asabar kuma shugaban da kansa ya yi kira da ECOWAS ta dage jingine tattalin arzikin da ta kakabawa kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso da Guinea.
A cewarsa, an sanya takunkumin ne da nufin shawo kan shugabannin gwamnatocin sojin kasashen zuwa teburin tattaunawa.
Ya bayyana cewa kungiyar ta dauki matakinta ne bisa kyawawan manufofin yankin na tsaro, zaman lafiyar al’umma, mulkin dimokuradiyya, ’yancin siyasa, yalwar arziki da ci gaban tattalin arziki mai dorewa ta hanyar samar da dama ga kowa a yammacin Afirka.
Ya ce babu wata kiyayya ko boyayyar manufa a cikin matakan da aka dauka kuma babu wata manufa ta ruguza halastacciyar manufar siyasa ta kowace kasa ko cigaban wani bangare.
Da haka ne Tinubu ya bukaci kungiyar da ta saukaka shigar da kayayyakin abinci da magunguna da sauran kayayyakin jin kai ba tare da katsewa ba ga al’ummar wadannan kasashe, musamman ma wadanda suka fi kowa rauni.