Najeriya ta nemi taimakon Faransa kan matsalar tsaro

Muna buƙatar dakile ayyukan masu garkuwa da mutane da sauran masu tayar da kayar baya a sassan kasar nan.

Najeriya ta nemi taimakon Faransa kan matsalar tsaro

Ministan Tsaron Najeriya Alhaji Muhammad Badaru Abubakar. (Hoto: Twitter/@HQNigerianArmy)

Gwamnatin Tarayya ta miƙa kokon bara na neman taimako da haɗin kan Faransa domin kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta dabaibaye kasar.

Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ne ya bayyana hakan yayin wata ganawar sirri da ya yi da wasu ’yan majalisa da kuma jami’an hukumomin tsaron Faransa a Yammacin wannan Talatar.

Ministan a yayin taron wanda Gassillound Thomas ya jagoranci wakilan Faransa a Abuja, ya buƙaci su kawo wa Najeriya ɗauki domin dakile ayyukan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da sauran kalubalen tsaro da suka addabi kasar.

A cikin sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Najeriya, Henshaw Ogubike ya fitar, ministan ya ce akwai bukatar a inganta alakar da ke tsakanin Najeriya da Faransa ta fannin kayan aikin soji da horar da jami’an sojin kasar.

“Ina da yakinin cewa Gwamnatin Faransa za ta iya tallafa wa Najeriya da kayan aiki domin dakile matsalar tsaro da tada kayar baya.

“Kun dai sani cewa Najeriya tana da dimbin al’umma da saboda haka idan akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali, tarin al’umma zai taimaka mana wajen bunkasar tattalin arziki,” kamar yadda Ogubike ya ruwaito Ministan na cewa.

Badaru ya ce Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu za ta yi amfani da hanyoyin da suka dace wajen ganin ta kawar da makiya da ke tayar da kayar baya a sassan kasar nan.

Tsohon Gwamnan na Jihar Jigawa ya kara da cewa, tun bayan zamansa ministan tsaro, ya yi ganawa har sau uku da Faransa a fannin hadin gwiwar soji, yana mai cewa “wannan yana nuna kyakkyawar alakar da muke da ita da Faransa”.

Ya kuma yaba wa dangantakar da ke tsakanin majalisar dokokin Faransa da ta Najeriya, inda ya ce irin wannan hadin kan zai bunkasa yaki da matsalar tsaro.

Da yake jawabi, Shugaban Majalisar Faransa, Mista Gassiloud Thomas, ya ce gwamnatinsu za za ta tallafa a wasu fannonin da Ministan Tsaro ke ganin gwamnatin Faransa za ta iya taimaka wa Najeriya wajen yaki da matsalar tsaro.

“Tabbas muna yabawa da rawar da kuke takawa wajen karfafa dangantakar, kuma za mu ci gaba da tallafa wa wannan gwamnati mai ci domin dakile matsalar tsaro.

“Wannan alakar tana da matukar muhimmanci domin Najeriya na da tasirin gaske dangane da irin rawar da take takawa wajen dakile matsalar nahiyyar Afirka.”

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja