Najeriya ta rasa biliyan $3 kan safarar zinare
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa kan yadda Najeriya ta yi asarar kusan Dala biliyan uku sakamakon sumogar zinare daga shekarar 2012 zuwa 2018. Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin wani biki a Fadar Shugaban Kasa don gabatar da wasu zinarai na gida a hukumance. Buhari ya ce baya ga kokarin samar […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa kan yadda Najeriya ta yi asarar kusan Dala biliyan uku sakamakon sumogar zinare daga shekarar 2012 zuwa 2018.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin wani biki a Fadar Shugaban Kasa don gabatar da wasu zinarai na gida a hukumance.
Buhari ya ce baya ga kokarin samar da ayyukan yi da kudaden shiga ga kasa ta fuskar ma’adinai, gwamnatinsa na kuma kokari wajen kafa masana’antun ma’adinai.
Ya ce, “Da zarar shirinmu na bunkasa harkar ma’adinai ya fara aiki, za mu kafa cibiyoyin cinikayyarsu a muhimman guraren da ake hako su wanda hakan kuma zai bunkasa kudaden shigarmu.
“Hakan zai kuma kara yawan kudaden ajiyarmu a kasashen ketare ta hanyar ba Babban Bankin Najeriya (CBN) zai kara yawan zinaren da yake a ma’ajiyarsa”, inji Buhari.
A kan batun tabbatar da lafiyar wuraren hakar ma’adinai, shugaban ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun dauki matakan kariya don kare ingancin muhalli da kuma lafiyar masu hakan.
Ya kuma ce gwamnatinsa za ta tallafa wa harkar ma’adinan ta hanyar samarwa da masu harkar rance domin inganta ta.