Najeriya ta rasa kwararren matukin jirgin ruwa a hadarin mota

Wani kwararren matukin jiragen ruwa da ya yi fice a duniya, mai suna Kyaftin Shehu Usman Jibrin ya rasu a wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da su a kusa da garin Kafanchan a  Jihar Kaduna, a hanyarsa ta zuwa Jos, bayan ya taso daga Abuja. Lamarin ya faru ne a yammacin ranar Lahadin […]

Najeriya ta rasa kwararren matukin jirgin ruwa a hadarin mota

Wani kwararren matukin jiragen ruwa da ya yi fice a duniya, mai suna Kyaftin Shehu Usman Jibrin ya rasu a wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da su a kusa da garin Kafanchan a  Jihar Kaduna, a hanyarsa ta zuwa Jos, bayan ya taso daga Abuja.

Lamarin ya faru ne a yammacin ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda Aminiya ta samu labari.

Da yake yi wa wakilinmu bayanin yadda hadarin ya faru, a gidansu da ke garin Jos, wani da ga marigayin kuma ma’aikaci a Ma’aikatar Tsaro ta Kasa, mai suna Aliyu Jibrin ya ce a ranar Lahadin da misalin karfe 5:00 na yamma ne suka samu labari daga Kafanchan cewa wata motar kirar Sharon mai launin ja, da ta taso daga Abuja zuwa Jos ta yi hadari a garin, kuma mutanen da ke cikin motar su 8, duk sun rasu.

Ya ce nan take suka sanar da sojoji a Kafanchan wadanda suka je wajen suka gano gawar marigayin da sauran fasinjojin.

Aliyu Jibrin ya ce sai suka tashi mutane daga Jos, suka tafi asibiti a can suka karbo gawar marigayin suka kawo ta Jos, inda a ranar Litinin da misalin karfe 10:30 na safe aka yi masa jana’iza.

“Gaskiya mun yi asara saboda rasuwar marigayin, domin mutum ne mai addini kuma mai saukin kai. A rayuwarsa ya je kasashen duniya sama da 30, a matsayinsa na matukin jirgin ruwa. Amma hakan bai sa ya canja halinsa ba.

Yana mu’amala da mutanen da suka taso tare. Saboda halinsa na rashin girman kai, yana da motocin hawa sama da biyar, amma ya ki ya shigo motarsa, ya je tasha ya shiga motar fasinja suka taho tare da sauran fasinjoji,” inji shi.

Da yake bayani kan tarihin marigayin, Aliyu Jibrin ya ce an haifi marigayin ne a Jos fiye da shekaru 50 da suka gabata.

Ya ce marigayin ya yi makarantar firamare ta St Paul a ’Yan Kaji da ke Jos. Daga nan ya wuce Sakandaren Gwamnati ta Kafin Hausa da Sakandaren Kimiyya da Fasaha ta Dawakin Kudu duk a tsohuwar Jihar Kano.

Aliyu ya ce daga nan ne marigayin ya tafi Makarantar Koyon Tukin Jiragen Ruwa da ke Oron a Jihar Akwa Ibom. Kuma daga baya ya samu gurbin karo karatu a wata makarantar koyon tukin jiragen ruwa a kasar Austireliya, kuma ya yi digiri na daya da na biyu kan tukin jiragen ruwa.

Ya ce marigayin ya yi aiki da wani kamfanin jiragen ruwa a kasar Amurka. Daga nan ya dawo Najeriya, ya kama aiki da Kamfanin Gas na Najeriya (LNG), har zuwa lokaci da Allah Ya karbi ransa.

Marigayin ya rasu ya bar matarsa Maryam da ’ya’ya uku maza biyu da mace daya, kuma an yi jana’izarsa kamar yadda Musulunci ya tanada a garin Jos.

An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo