Najeriya ta rufe iyakokinta ga matafiya daga Amurka da wasu kasashen

Gwamnatin Najeriya ta haramta shigowa kasar ga matafiya daga kasashe 13 na duniya, ta kuma dakatar da tsarin bayar da izinin shigowa (wato visa) a filin jirgin sama, sakamakon dakile yaduwar cutar kurona. Kasashen da aka rufe wa kofar sun hada da: Amurka da Birtaniya da China da Italiya da Iran. Sauran sun hada da: […]

Najeriya ta rufe iyakokinta ga matafiya daga Amurka da wasu kasashen

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha

Gwamnatin Najeriya ta haramta shigowa kasar ga matafiya daga kasashe 13 na duniya, ta kuma dakatar da tsarin bayar da izinin shigowa (wato visa) a filin jirgin sama, sakamakon dakile yaduwar cutar kurona.

Kasashen da aka rufe wa kofar sun hada da: Amurka da Birtaniya da China da Italiya da Iran.

Sauran sun hada da: Koriya ta Kudu da Sipaniya da Japan da Faransa da Jamus da Holand.

Sai kuma Norway da Switzerland.