Najeriya ta sa sabbin ka’idoji bude makarantu
Gwamnatin Tarayya ta gindaya sabbin sharuddan bude makarantu a fadin Najeriya bayan sabanin da ake samu a kasar kan bude makarantun ga dalibai masu jarabawar kammala sakandare. Gwamnatin wadda ta ce ba za ta bude makarant ba sai an tabbatar da amincin dalibai daga cutar coronavirus, ta ce sabbin sharuddan da ma’aikatun ilimi, lafiya da […]
Gwamnatin Tarayya ta gindaya sabbin sharuddan bude makarantu a fadin Najeriya bayan sabanin da ake samu a kasar kan bude makarantun ga dalibai masu jarabawar kammala sakandare.
Gwamnatin wadda ta ce ba za ta bude makarant ba sai an tabbatar da amincin dalibai daga cutar coronavirus, ta ce sabbin sharuddan da ma’aikatun ilimi, lafiya da muhalli suka fitar za su taimaka a bude makarantun cikin tsaron lafiya.
“COVID-19 babbar barazana ce ga lafiyar dalibai, malamai, iyaye, masu kula da makarantu, masu harkar ilimi da ma ala’umma… a matsayin gwamnatin da ta san abin da ya dace, aikinmu ne samar da tsarin tabbatar da aminci kafin sake bude makarantu da sauran cibiyoyin ilimi”, inji Ministan Ilimi, Adamu Adamu.
Dokokin da ministan ya sanya wa hannu sun hada da fitar da tasrin halartar makaranta, bayar da tazara, tsaftar muhalli da kuma sauya tsarin amfani da makarantu domin wasu harkokin.
Rahoton ce muddin ba za a bayar da tazanar mita biyu to wajibi ne a dauka matakan kariya ga dalibai da malamai da sauran ma’aikata.
“Hakan zai bukaci tara dalibai a kananan rukuni-rukunin da babu sauyi a ciki, tare da kiyaye uk wata barazana, kuma dole ya dace da ka’idojin kariya na hukumar NCDC’, inji sanarwar.
Bayan rufe makarantu a narar tara ga watan mariya, Karamin Ministan Lafiya Chukwuemeka Nwajiuba, a cikin wantan Yuni ya sanar da wasu sharudda guda shida kafin saar da bude makarantu.
Ya ce kafin a sake bude makarantu dole ne kowace makaranta ta samar da wadannan abubuwa:
- Samar da kayayyakin wanke hannu.
- Auna zafin jiki.
- Kashe kwayoyin cuta a daukacin jiki a dukkannin kofofin shiga azuzuwa, ofisoshi, dakunan kwanan dalibai da sauransu.
- Kashe kwayoyin cuta a ko ina a fadin makarantar.
- A yi iya kokari wurin tabbatar da kula da kuma kare lafiya.
- Tabbatar da bayar da kariya a azuzuwa da ofisoshi da zauran wurare.
Duk da haka Ministan ya gargadi makarantu da su guji budewa ba tare da samun izinin yin hakan daga Gwamnatin Tarayya ba.
“Yayin da muke kokarin sassauta dokar kulle da zai kai ga bude makarantu, ina kira ga dukkan shugabannin makarantu kada su jira sai an sanar da sake bude makarantu kafin su ce za su dauki matakan da suka dace na bin ka’idodi da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta shimfida.”