Najeriya ta samu harajin Naira biliyan 275.12– NBS

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta ce Najeriya ta tara Naira biliyan 275.12 a tsakanin watan Yuli zuwa Satumban bana. Wannan adadin kudi bai kai yawan wadanda aka tara a tsakanin watan Afrilu zuwa Yunin bana ba. A wani rahoto da jaridar Premium Times ta wallafa a shafinta na Intanet, ya nuna cewa an samu […]

Najeriya ta samu harajin Naira biliyan 275.12– NBS

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta ce Najeriya ta tara Naira biliyan 275.12 a tsakanin watan Yuli zuwa Satumban bana.

Wannan adadin kudi bai kai yawan wadanda aka tara a tsakanin watan Afrilu zuwa Yunin bana ba.

A wani rahoto da jaridar Premium Times ta wallafa a shafinta na Intanet, ya nuna cewa an samu koma baya idan aka yi la’akari da kudin da aka tara  a watan Afrilu zuwa Yuni, da ya kai Naira biliyan 311.94 a matsayin kudaden harajin ‘BAT’ na wancan lokaci.

Hukumar NBS ta fitar da wannan sanarwar ce a ranar Litinin da ta gabata a Abuja, lokacin da ta fitar da bayanan kudin da ake tarawa a duk wata uku.

Ana daukar tsawon wata uku ana tarawa, sannan a bayyana abin da aka samu.

Haka rahoton ya tantance cewa a tsakanin Yuli zuwa Satumban bara, an tara Naira biliyan 273.50.

Idan ba a manta ba, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci masu sarrafa harkokin tattalin arzikin Najeriya su nemo hanyoyin kara samun kudaden shiga a kasar nan.

Ya ce za a rika biyan albashi da kudin, maimakon a rika fita kasashen waje ana ciwo bashin da za a rika biyan albashi duk karshen wata. A kan haka ne aka bijiro da karin harajin BAT, daga kashi 5 zuwa kashi bakwai da rabi cikin 100.

Wannan na nufin nan da dan lokaci kadan harajin BAT zai karu sosai.

Hukumar NBS ta ci gaba da bayyana bangarorin da aka fi samun kudaden shiga, wato haraji daga wurinsu, inda ta ce an samu mafi yawan kudin ne a bangaren ayyukan yau da kullum da kayan dinkin tufafi da masana’antun yin tufafi da  magunguna da sabulai da sauran nau’o’in kayan ban-daki da sauransu.