Najeriya ta samu karin yawan kayan da take fitarwa
Kasar Najeriya ta samu karin yawan kayan da take fitarwa kasashen waje inda kayan amfanin gona ya kara wa kasar kudin shiga. Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayar da rahoton cewa kayan da Najeriya take fitarwa ya karu da kashi 73 da digo biyar cikin dari a zagon shekar na biyu idan aka kwatanta […]

Kasar Najeriya ta samu karin yawan kayan da take fitarwa kasashen waje inda kayan amfanin gona ya kara wa kasar kudin shiga.
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayar da rahoton cewa kayan da Najeriya take fitarwa ya karu da kashi 73 da digo biyar cikin dari a zagon shekar na biyu idan aka kwatanta da zagon shekara na farko na shekarar da ta gabata.
Masana sun alakanta karin da aka samu a kan shirin gwamnati na mayar da hankali kan albarkatun da ba na mai ba.