Najeriya ta sanar da ranakun hutun Kirsimati da sabuwar shekara

Gwamnatin tarayyar  Najeriya ta sanar da ranakun 25 ga watan Disamba da 26 wato Laraba da Alhamis da kuma 1 ga Janairun 2020 a matsayin hutun Kirsimati da kuma na sabuwar shekara. Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Barista Georgina Ehuriah ya fitar a madadin gwamnatin […]

Najeriya ta sanar da ranakun hutun Kirsimati da sabuwar shekara

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola

Gwamnatin tarayyar  Najeriya ta sanar da ranakun 25 ga watan Disamba da 26 wato Laraba da Alhamis da kuma 1 ga Janairun 2020 a matsayin hutun Kirsimati da kuma na sabuwar shekara.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Barista Georgina Ehuriah ya fitar a madadin gwamnatin tarayya.

Sanarwar ta kara da cewa, Ministan ya taya Kiristoci da kuma ‘yan Najeriya murna da kuma yin kira da zauna lafiya yayin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.