Najeriya ta soke harajin VAT a kan iskar gas da man dizel

Wannan na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Najeriya na rage dogaro da man fetur a ƙasar

Najeriya ta soke harajin VAT a kan iskar gas da man dizel

Gwamnatin Tarayya ta soke karɓar harajin VAT a kan iskar gas da man dizel da dangoginsu.

A kokarinta na sauƙaƙa tsadar sufuri da rage dogara da ababen hawa masu amfani da man fetur ne gwamantin ta soke harajin VAT a kan waɗannan nau’ikan mai.

Wannan na daga cikin ƙoƙarinta gwamnati na karya farashin makamashi a ƙoƙarinta na bunƙasa amfani da ababen hawa masu amfani da gas ɗin CNG da LNG da man dizel da kuma wutar lantarki.

Karin bayani na tafe.