Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Peter Obi

Najeriya ba ta ci gaba ba kamar takwarorinta daga 1992 lokacin da IBB ya bar gwamnati.

Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Peter Obi

Peter Obi

Dan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar Leba (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce Najeriya ta daɗa taɓarɓarewa fiye da lokacin da tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja Ibrahim Badamasi Babangida ya bar mulki a shekarar 1992.

Obi ya bayyana haka ne a lokacin da yake tsokaci kan ƙaddamar da littafin tarihin Babangida da aka daɗe ana jira, mai suna ‘A Journey in Service’.

Aminiya ta gano cewa, ba a ba wa Obi damar shiga ba cikin zauren taron ƙaddamar da littafin ba, tare da wasu da dama da aka yi zauren taro na Congress Hall a otal din Transcorp Hotel, inda aka gudanar da taron saboda an kulle ƙofofin shiga bayan isowar Shugaba Bola Tinubu.

Obi, a saƙonsa da ya wallafa a shafin sada zumunta na X, ya bayyana cewa irin gudunmawar da IBB ke bayarwa ga tattalin arzikin Najeriya da gagarumin goyon bayansa ga harkokin kasuwanci da bunƙasar kamfanoni masu zaman kansu ba su da iyaka.

Da yake magana a kan abin da ya kira wasu muhimman abubuwa guda biyu na jawabin da IBB ya yi game da zaɓen 1993, ya ce Najeriya ba ta ci gaba ba kamar takwarorinta daga 1992 lokacin da IBB ya bar gwamnati.