Najeriya ta talauce – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hakikance cewa kasar nan ta talauce kuma bai ga dalilin da zai sa ya yi karya dangane da halin da tattalin arzikin kasar nan yake ciki ba. Ya ce dole ne a fada wa duniya gaskiyar halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki, domin masu zuba jari suna sane da […]

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hakikance cewa kasar nan ta talauce kuma bai ga dalilin da zai sa ya yi karya dangane da halin da tattalin arzikin kasar nan yake ciki ba.
Ya ce dole ne a fada wa duniya gaskiyar halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki, domin masu zuba jari suna sane da halin da kasar ke ciki.
Har ila yau, Shugaban ya ce zai nada ministoci 36 ne kamar yadda kundin tsarin mulki ya bukaci ya yi. Ya bayyana hakan ne lokacin da Shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki ya kai masa sunayen ministoci da majalisar ta tantance.
Sanata Saraki ya isa fadar shugaban kasar ne bisa rakiyar Masu Taimaka wa Shugaban kasa Kan Harkokin Majalisa wato Sanata Ita Enang da kuma Suleiman Kawu, a ranar Talata.
Shugaba Buhari ya fara ayyana cewa kasar nan ta talauce ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin New Delhi na kasar Indiya. Ya ce kasar nan tana fama da kalubalen biyan albashin ma’aikata. Saboda bayyana gaskiyar halin da kasar nan take ciki ya sa jam’iyyar adawa ta PDP ta fara Allah-wadai da kalaman shugaban.
Kodayake, a lokacin ganawar ya ce yana so a tuna da shi a matsayin shugaban Najeriya da ya ci nasara kan matsalar cin hanci da rashawa, duk da haka ya bukaci jama’ar kasar nan wadanda ba su azurta kansu da dukiyar al’umma ba da kada su ji tsoron komi.
Har ila yau, ya ce ya zama wajibi ya rage yawan ma’aikatun gwamnatin tarayya domin ya samu damar biyan albashi.
Da yake mayar da martani ga masu sukarsa game da yadda yake tafiyar hawainiya wajen maganin matsalolin kasar nan, shugaban ya ce, “suna kirana da sunan Baba mai tafiyar hawainiya, amma ni zan ci gaba da tafiyata ne a hankali cikin nutsuwa.”
Daga nan sai ya yi kira ga manya a cikin al’umma da su hada hannu da shi don hukunta da duk wanda ya ci amanar da aka danka masa.
Bugu da kari, ya ce abubuwa uku da gwamnatinsa za ta fi mayar da hankalinta a kai su ne: tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa. Sai dai jam’iyyar adawa ta PDP tana sukarsa da cewa yana nuna son kai a yaki da cin hanci da rashawa.
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi tun cikin watan Mayun da ya gabata ya sha nanata cewa kasar ta talauce, inda yake dora alhakin rashin biyan albashin ma’aikata da ’yan fanshon kasar kan halin da kasar ta samu kanta a ciki na karancin kudi.
Tsohon Gwamnan ya ce an taba kiransa da sunan mai yawan ruruta al’amura a bara, lokacin da ya hangi matsalar karancin kudin da kasar nan ta kama hanyar fadawa. Mista Amaechi ya ce tun daga watan Disambar bara lokacin da ya yi hangen nasa, tattalin arzikin kasar nan ya ci gaba da samun koma baya.
“A bara lokacin da na ce tattalin arzikin Najeriya yana kan siratsi, wasu cewa suka yi ina so in cusa tsoro a zukatan jama’a. Amma tun daga wancan lokacin zuwa yau al’amura baya suke yi ba gaba ba. Yanzu ka ga kusan duka jihohin kasar nan da kyar suke iya biyan albashin ma’aikata,” inji shi.
Kana bata sunan kasarmu ne -PDP
A wani martani da jam’iyyar PDP ta mayar kan batun ta bakin Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar, Cif Oliseh Metuh, cewa ya yi ya kamata Shugaba Buhari ya bar cusa tsoro a zukatan masu zuba jari, ta hanyar abin da ya kira, “bata sunan kasar nan” da bayyanata ta fuskar da “ba ta dace ba da kuma tattalin arzikinta,” inji shi.
Jam’iyyar PDP ta ce watanni shida da suka gabata na gwamnatin APC, “Buhari ya yi amfani da su ne wajen kashe kasuwar kasar nan a idon masu zuba jari daga kasashen ketare, a madadin ya yi kokarin bunkasa albarkatun kasar nan wajen ciyar da tattalin arzikinta gaba.”
Hakazalika, tsohon Ministan Sufuri da Zirga-zirgar Jiragen Sama, Ebenezer Babatope, ya ce bai dace Shugaba Buhari ya ce kasar ta talauce ba. Mista Babatope wanda Mamba ne a Kwamitin Amintantu na Jam’iyyar PDP, ya ce “jam’iyyar adawa da kuma ’yan Najeriya za su ga yadda shugaban kasar zai magance matsalar tattalin arzikin da surutan da jam’iyyar APC take yi lokacin da aka gudanar da zabe.”
Ya ci gaba da cewa: “A matsayina na dalibin marigayi Obafemi Awolowo a siyasance. Ba zan taba yarda da cewa Najeriya ta talauce ba saboda shugabana (Awolowo) ya ce babu wata kasa da za ta talauce, sai dai idan ta kasa sarrafa albarkatunta don ci gabanta da kuma bunkasarta.”
A karshe ya ce: “Tun da Shugaba Buhari ne yake jagorantar al’amuran kasar nan a yanzu, idan ya ce kasar nan ta talauce, abin ya yi muni kwarai.”