Najeriya ta yi asarar Dala biliyan 15 a badakalar makamai lokacin Jonathan – Osinbajo
Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce Najeriya ta yi asarar Dala biliyan 12 (kimanin Naira tiriliyan 2 da biliyan 955 a musayar gwamnati ko Naira tiriliyan 4 da biliyan 830 a kasuwar bayan fage) sakamakon cuwa-cuwa da almundahan wajen sayo sayo kayayyakin yaki a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan da ta gabata.FarfesaYemi Osinbajo ya […]
Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce Najeriya ta yi asarar Dala biliyan 12 (kimanin Naira tiriliyan 2 da biliyan 955 a musayar gwamnati ko Naira tiriliyan 4 da biliyan 830 a kasuwar bayan fage) sakamakon cuwa-cuwa da almundahan wajen sayo sayo kayayyakin yaki a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan da ta gabata.
FarfesaYemi Osinbajo ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da yake kaddamar da wani littafi mai suna “Najeriya: kalubalen Bunkasa da Ci gaba,” a harabar Jami’ar Ibadan a Jihar Oyo.
Mataimakin Shugaban kasar ya ce kasar nan ba za ta iya jure mugun cin hanci da almundahana da ke addabar hukumomin gwamnati ba. “Idan kuka kalli dimbin kudin da suka almubazzarantar da dimbin kudin da aka yi asara daga irin wadannan miyagun cin hanci da aka tafka, za ku ga an yi mummunar asara,” inji shi.
Ya kara da cewa: “A ’yan kwanakin nan an gano jimillar kudin da aka yi asara a bangaren tsaro da samar da kayayyakin yaki ga sojoji ya yi kusan kai Dala biliyan 15,” inji Farfesa Osinbajo kamar yadda kakakinsa Laolu Akande ya fadi a wata sanarwa.
Farfesa Osinbajo ya ce adadin “ya fi rabin kudin ajiyar kasar nan a yanzu,” a yanzu Najeriya tana da ajiyar waje Dala biliyan 27 ne.
Ya shaida wa mahalarta taron wadanda suka hada da ’yan Bokon Najeriya da suka fito daga cibiyoyin ilimi da fannonin kasuwanci da sana’o’i cewa kokarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari take yi shi ne “ta tabbatar akwai ukuba ga duk wata almundahana, kuma muna kokarin aikewa da sako cewa duk wanda aka samu da almundahana ba ma za a kwace dukiyar da ya sace kadai ba ne, har sai sun dandana kudarsu ta wajen hukunta su kamar yadda doka ta tanada,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Ina da cikakken yakini cewa yana da muhimmanci a aike da sakon cewa babu wani ma’aikaci da zai iya satar dukiyar kasar nan amma ya sa ran zai sha. Ina fata wannan sako zai shiga kunnen jama’a sosai ta yadda za a samu gyara a nan gaba.”
Farfesa Osinbajo ya ce abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a Najeriya sun nuna “yadda ’yan book suka yi nesa da kyawawan halaye. Maimakonsu suka rungumi dukkan halaye na neman uzuri da karairayin kare munanan dabi’u. Yau ana amfani da kabilanci da addini wajen kare almundahana da cin hanci. Ana karfafa aikata ba daidai bat a hanyar danne inganci ta hanyar tsarin raba-daidai. Tsarin raba-daidai a zahirinsa ba laifi ba ne, amma ya zamo bisa cancanta ba ya zama tilas ba,” inji shi.
Mataimakin Shugaban kasar ya ce za a fara aiwatar da kasafin kudin bana wanda ya bayyana da mafi buri ga Najeriya nan da ’yan kwanaki kadan.