Najeriya ta yi rashin Dokta Aled Ekwueme

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Dakta Aled Ekwueme ya rasu a wani asibiti a birnin Landon ranar Lahadin da ya gabata, bayan da ya yi fama da doguwar rashin lafiya wanda ya hada da daukewar numfashi akai-akai. Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da dan uwansa kuma Babban Basaraken Oko dake Jihar Anambra, Farfesa Laz Ekwueme […]

Najeriya ta yi rashin Dokta Aled Ekwueme

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Dakta Aled Ekwueme ya rasu a wani asibiti a birnin Landon ranar Lahadin da ya gabata, bayan da ya yi fama da doguwar rashin lafiya wanda ya hada da daukewar numfashi akai-akai. Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da dan uwansa kuma Babban Basaraken Oko dake Jihar Anambra, Farfesa Laz Ekwueme ya fitar a yanmacin ranar.

Marigayin mai shekaru 85 ya rasu ne kwanakin kadan bayan umarnin da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayar na duba lafiyar tsohon mataimakin shugaban kasar a karkashin kulawar gwamnati a kasar waje.

Matakin ya biyo bayan bayanan da shugaban ya samu ne game da halin jinyar da yake ciki. Inda gwamnatin ba shi jirgin da zai kai shi da kuma kudin maganin da za a yi masa a can.

An haifi Aled Ifeanyichukwu Ekwueme ne a ranar 21 ga watan Oktobar shekarar 1932.Ya fara makarantar furamare a John Angilika dake garin Ekulobia. Daga nan kuma ya zarce makarantar sakandare ta King’s College dake Legas.

Ya samu tallafin karatu na Fulbright domin yin karatun digiri a Amurka, ya fara karatun nasa a jami’ar Washington, inda ya samu digiri a fannin gine-gine da tsara birane. Haka kuma ya samu digirinsa na biyu a fannin tsara birane. Sannan ya garzaya jami’ar Strathclyde domin karatun digiri na uku a fannin gine-gine.

Haka zalika ya yi karatun digiri a fannin shari’a a makarantar horar da lauyoyi ta Najeriya. Sannan mutum ne da ya yi fice a aikinsa na zane-zane. Ya fara aikinsa na tsara gine-gine ne da wani kamfani da ke Seattle, Leo Daly and Associates, sannan kuma ya yi aiki da kamfanin Nickson and Partners da ke Landon.

Da ya dawo Najeriya, ya koma kamfanin ESSO West Africa, inda ya jagoranci fannin gine-gine da gyare-gyare. Daga nan ne Aled ya kafa wani kamfani na kansa, Ekwueme Associates, Architechs and Town Planners, kamfani irinsa na farko da aka fara kafawa a Najeriya.

Aikinsa ya ci gaba a Najeriyar har ya bude ofisoshi kimanin 16 a sassan kasar nan daban-daban. Sai dai kuma kafin ya zama mataimakin shugaban kasa a shekarar 1979, marigayin ya rufe kamfanin nasa domin samun damar ayyukan shugabanci.

Ya fara siyasa ne da shiga jam’iyyar NPN wadda ta tsayar da Alhaji Shehu Shagari da shi Aled Ekwueme a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa a shekarar 1979, kuma suka yi nasara a zaben, inda suka shafe kimanin shekara hudu suna mulkin Najeriya.

Bayan sun gama wa’adinsu na farko, sai kuma suka sake lashe zaben wa’adi na biyu, sai dai kuma sojoji sun hambarar da gwamnatin tasu a Watan Disambar shekarar 1983 bayan watanni uku kacal da fara wa’adi na biyun. 

To amma a lokacin juyin mulkin, Aled Ekwueme na cikin mukarraban gwamnatin da aka daure a kurkuku karkashin gwamnatin mulkin soja ta Janar Buhari bisa zargin cin hanci da rashawa. Amma da Janar Ibrahim Babangida ya hambarar da gwmanatin Buhari, an fitar da shi daga kurkuku, inda aka yi masa daurin talala.

Sannan daga baya an sassauta daurin daga kebe shi cikin gida zuwa karamar hukuma. Daga baya kuma, a shekarar 1989, aka ce kada ya fice daga Najeriya. Sai dai kuma ya samu damar fita daga Najeriya bayan shekara shida.

Marigayi Aled Ekwueme ya shiga cikin ‘yan siyasa wadanda suka yi fafatukar neman tsohon shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha da ya jingine aniyarsa ta zarcewa daga soja zuwa farar hula.

Shi da ‘yan siyasa da masu fafatikar tabbatar da dimokuradiyya a kasar nan sun gabatar da bayanai da ke nuna bukatunsu na hana tazarce da kuma komawar Najeriya tafarkin dimokuradiyya.

Aled Ekwueme na cikin wadanda suka kafa babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya PDP, haka kuma ya na cikin wadanda suke fafatukar neman a sauya fasalin kasar.

A taron tsara kundin tsarin mulki na Najeriya wanda ya haifar da kundin tsarin mulkin shekarar 1999 da ake amfani da shi yanzu a kasar, Ekwueme ne ya raba Najeriya zuwa yankuna shida a siyasance.

Yankunan da suka hada da Arewa maso Yammaci da Arewa maso Gabashi da Arewa ta tsakiya da Kudu maso Kudanci da Kudu maso Yammaci da kuma Kudu maso Gabashin Najeriya.

Duk da cewa shawarar da ya bayar na tsarin mulkin karba-karba tsakanin yankunan na Najeriya bai samu karbuwa ba, shawarar tasa ta zama ginshikin yankuna siyasar Najeriya shida da ake amfani da su wajen raba arzikin kasa da sauran al’amura.