Najeriya ta yi wa Palasdinu kafar-ungulu
Kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin Duniya ya yi watsi da wani daftarin kudurin Palasdinawa da kasar Jordan ta gabatar wa kwamitin, wanda ya yi kira da a kawo karshen mamayar da Isra’ila take yi a yankin Palsdinu a shekara uku da suka gabata.Wannan kuduri bai samu kuri’a tara da ake bukata ba, saboda kasashe takwas […]
Kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin Duniya ya yi watsi da wani daftarin kudurin Palasdinawa da kasar Jordan ta gabatar wa kwamitin, wanda ya yi kira da a kawo karshen mamayar da Isra’ila take yi a yankin Palsdinu a shekara uku da suka gabata.
Wannan kuduri bai samu kuri’a tara da ake bukata ba, saboda kasashe takwas ne suka aminta da kudurin, sannan biyar suka kaurace wa zaben ciki har da Najeriya. Da Najeriya ta goyi bayan kudurin kamar yadda aka ce Shugaba Jonathan ya yi akkawari, da kasar Palasdinu ta haye. Wannan matsayin da Najeriya ta dauka an ce ya yi wa Shugaban Isira’ila Natanyaho dadi har ya yi wa Shugaba Jonathan godiya.
To, sai dai kasar ta Jordan ta ce kuri’ar da aka kada, ba za ta dakatar da yunkurin da ake na warware rikicin ba.
Koda an samu kasashe tara sun amince da kudirin Amurka tana iya amfani da matsayinta na hawa kujerar na ki don dakatar da kudirin.
Jakadiyar Amurka a majalisar Samantha Power ta ce ba sun jefa kuri’ar rashin amincewa da kudirin ba ne, saboda sun gamsu da halin da ake ciki ba, sun yi haka ne domin zaman lafiya ya samu ta hanyar hawa teburin shawara.
Daga cikin wakilai 15 na kwamitin kasashen Rasha da China da Ajentina da Chadi da Chile da Jordan da Luzembag sun goyi bayan kudirin, yayin da Amurka da Autireliya suka ki, sannan Ingila da Lituweniya da Najeriya da Jamhuriyyar Koriya da Rwanda suka kaurace wa jefa kuri’ar.
Tuni Firayi Ministan kasar Isra’ila Benjamin Natenyahu ya yaba wa Shugaban kasa Goodluck Jonathan kan kin jefa kuri’ar da Najeriya ta yi, wanda hakan ne y aba Isra’ila nasara kan wannan batu.
Natenyahu ya ce ya yi waya da Shugaba Jonathan don nuna godiyarsa kan wannan karimci da Najeriya ta yi.