Najeriya ta zama takalmin kaza, mutu-ka-raba

A ’yan kwanakin nan ana ta samun barazana daga kungiyoyin yankunan kasar nan inda har ya kai ga yin kira ga ’yan Arewa da ke yankin Gabashin kasar nan su  koma gida Arewa idan suka ga matsin ya yi yawa. Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo ne ya kara ruruta wutar tunzurin da ake yi na barka […]

Najeriya ta zama takalmin kaza, mutu-ka-raba
Najeriya ta zama takalmin kaza, mutu-ka-raba

A ’yan kwanakin nan ana ta samun barazana daga kungiyoyin yankunan kasar nan inda har ya kai ga yin kira ga ’yan Arewa da ke yankin Gabashin kasar nan su  koma gida Arewa idan suka ga matsin ya yi yawa.

Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo ne ya kara ruruta wutar tunzurin da ake yi na barka Najeriya a yayin da ya bayyana cewa ana kokarin Fulatarwa da kuma Musuluntar da Najeriya. Wannan magana da ya yi ta haifar da muhawara kwarai, inda wadansu da dama da suka fito daga yankin Kudancin kasar nan da wadansu ’yan tsiraru daga yankin Arewacin kasar nan suka goyi bayansa.

Kafin wannan lokaci ana daukar tsohon Shugaban Kasa Obasanjo a matsayin cikakken dan kishin kasa da ya yi tsayuwar daka wajen ganin kasar nan ta ci gaba da zama dunkulalliya, amma abin mamaki sai aka wayi gari Obasanjo ya zama a kan gaba wajen ruruta wutar kabilanci da bambancin addini a kasar nan.

Masu fashin baki suna ganin Obasanjo ya yi wannan zargi ne domin ya haifar da rudani a kasar nan wanda zai sanya a kawar da hankali daga yunkurin binciken gwamnatinsa da za a yi game da Dala biliyan 16 da ta ce ta kashe wajen samar da wutar lantarki amma wutar ba ta samu ba. Saboda haka tunda Obasanjo ya ga Shugaba Buhari yana so ya farke masa laya, sai shi ma ya yunkura  ya ce ‘idan ka san wata, ba ka san wata ba,’ saboda haka sai ya sako wa gwamnatin Buhari kura, inda ya sake rubuta masa  budaddariyar wasika yana sukar gwamnatinsa da cewa ta gaza ta fuskar tsaro.

A cikin wasikar ce yake cewa ya yi Yakin Basasa domin tabbatar da hadin kan kasar nan kuma dansa na cikinsa yana dauke da raunuka a sakamakon yaki da Boko Haram da ake yi a yankin Arewa maso Gabas na kasar nan, yana dai so ya nuna cewa shi har yanzu mai kishin kasar nan ne.

Sai dai kuma mutane suna tababar cewa yana kishin kasar nan, domin idan haka ne ba zai ba Shugaban Kasa shawara ta hanyar budaddiyar wasika ba, zuwa zai yi Fadar Shugaban Kasa ya same shi ya ba shi shawara, domin a farkon gwamnatin Buhari Obasanjo yana zuwa wurinsa a Abuja su tattauna kan wasu al’amura, me ya sanya yanzu ya bari?

Ko ma dai mene ne dalilinsa, matukar yana kishin kasar nan ai bai kamata a wayi gari ya zama mai ruruta wutar kabilanci da bambancin addini ba, domin kasancewarsa Bayarbe akwai ’yan uwansa na jini da suke cikin addinin Musulunci, hasali ma har masallaci babba ya gina a Abeokuta, amma yanzu saboda ya lura gwamnati ba ta yi da shi sai ya gwammace ya tarwatsa kasar yadda kowa zai kama gabansa.

Ba abu ne mai sauki ba tarwatsewar Najeriya, domin tunda aka hada yakin Kudancin Najeriya da Arewacinta a 1914, wadansu ke ta kokarin su tarwatsa tafiyar, yunkurin hakan ya kara kamari ne lokacin da kasar nan ta samun ’yancin kanta daga Turawan Ingila, wadanda suka mika mulkin kasar ga ’yan Arewa, alhali ’yan Kudu suna ganin su ne ya kamata su mulki kasar nan domin su ne suke  da ilimin boko.

Wannan abu da Turawa suka yi ya kara ruruta wutar kiyaya a tsakanin ’yan Arewa da ’yan Kudu, kuma har yanzu kiyayyar tana nan, sai dai wani lokaci ta dan lafa, wani lokaci kuma ta taso da karfi kamar kasar za ta tarwatse, sai kuma abubuwa su lafa a ci gaba da tafiya tare.

Yanzu sabon salon da aka fito da shi shi ne na dora wa Fulani makiyaya kahon zuka ta yadda  duk inda suka shiga ake kyamatarsu, musamman a yankin Kudancin kasar  nan. Kuma saboda barazana ga rayukan Fulani makiyaya da dukiyoyinsu da ake yi ne ya sanya wadansu dattawa a yankin Arewa suka shawarci Fulanin su dawo gida Arewa tunda rayuwarsu na cikin hadari, amma sai aka yi ta sukar wannan shawara da dattawan suka bayar, daga cikin masu sukar har da Gwamnatin Tarayya.

Sai dai kuma wannan barazanar ta yi amfani, domin gwamnonin yankin Kudu maso Gabas sun fito fili sun nuna cewa ba su bukatar Fulani makiyaya su bar yankin nasu.

Saboda dadewa da aka yi ana zaune tare yanzu Najeriya ta cakude ta zama tamkar hatsin bara da zai yi wuya a iya rabe dawa da gero da nasara da waken da aka cakuda a kwarya daya. Domin yanzu yadda ake da Hausa Fulani a Arewacin kasar nan haka ake da Fulani Yoruba a yankin Kudu maso Yammacin kasar nan wadanda ba su jin Hausa sai Yarbanci da Fulatanci kawai. Haka kuma akwai Fulani Ibo wadanda su ma Fillanci da Ibo kawai suka iya.

A yankin Arewaci kuma akwai Yarbawa da yawa da suka yi auratayya da Hausawa suka rikide suka zama Hausawa ta yadda hatta ’yan uwansu Yarbawa ba za su taba yarda cewa asalinsu Yarbawa ne ba. Haka al’amarin yake da kabilar Ibo da ke zaune a yankin Arewa, inda za ka ga wani dan kabilar Ibo yana magana da harshen Hausa ba za ka taba yarda cewa Ibo ne ba, idan a yanki Adamawa ne za ka ga dan kabilar Ibo yana Fillanci kamar jakin Yola.

Wato yanzu ’yan Najeriya sun cakudu da juna ta yadda rabuwarsu za ta yi wahala, saboda harkokin kasuwa da addini da auratayya da sauran wasu manyan mu’amaloli sun hada su kuma an sanya sufa- gulu an manne su tare da dinke su da zare kirtani.

Saboda haka masu kuruwar tarwatsa kasar nan suna bata lokacinsu ne kawai domin rabuwar kasar nan ba abu ne mai sauki ba a yanzu. Su kansu Turawan mulkin mallaka da suka hada yankunan da aka samu kasar Najeriya ba su yi tsammanin Najriya za ta dinke irin haka ba.

Ga dukkan alamu dai Najeriya za ta ci gaba da zama dunkulalliyar kasa na tsawon lokaci saboda tsarinta ya bambanta da na sauran kasashen duniya. Domin akwai Bahaushe mai auren Bayarbiya, akwai Ibo mai auren Bahaushiya. Akwai wani tsohon Janar da mahaifinsa Ibo ne, mahaifiyarsa Bahaushiya, matarsa kuma Bayarbiya, to wannan idan an raba Najeriya ana za shi tare da ’ya’yansa? Najeriya dai ta zama takalmin kaza mutu-ka-raba.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos