Najeriya ta zama zakara a gasar kwallon kwando na Afirka

Babbar kungiyar wasan kwallon kwando ta kasa (Basketball) da ake kira D’tigers ce ta zama zakara a gasar kwallon kwando na Afirka da ya gudana a Tunisiya. kungiyar D’tigers ta samu nasara ce a kan ta Angola a wasan karshe da ci 65 da 74. Wannan dai shi ne karo na farko da Najeriya ta […]

Najeriya ta zama zakara a gasar kwallon kwando na Afirka
Najeriya ta zama zakara a gasar kwallon kwando na Afirka

Babbar kungiyar wasan kwallon kwando ta kasa (Basketball) da ake kira D’tigers ce ta zama zakara a gasar kwallon kwando na Afirka da ya gudana a Tunisiya. kungiyar D’tigers ta samu nasara ce a kan ta Angola a wasan karshe da ci 65 da 74. Wannan dai shi ne karo na farko da Najeriya ta taba lashe kofin a tarihin gasar.
Idan za a tuna an fitar da Najeriya daga irin wannan gasa ce a shekarar 2013 a matakin kwata-fainal.
Hakan ta sa kungiyar ta dauko hayar mai horar da ita daga Amurka mai suna Wil boights wanda ya yi amfani da kashi tamanin daga cikin 100 na ’yan kwallon da suka fafata a gasar a shekarar 2013 ga shi kuma ya samu nasara a wannan karo.
dan Najeriya Chamberlain Oguchi ne aka zaba a matsayin dan kwallon da ya fi kwazo a gasar yayin da aka zabi dan Senegal Gorgni Dieng a matsayin wanda ya fi iya zura kwallaye a raga.
Tuni ’yan kwallon suka koma Najeriya inda ake sa ran gwamnati za ta karrama su saboda tarihin da suka kafa a wasan kwallon kwando na Afirka.