Najeriya tana bukatar wayoyin masu tsawon kilomita dubu 120 don inganta sadarwar Intanet – Dambatta

Babban Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) Farfesa Umar Garba dambatta ya ce idan ana son cimma nasarar inganta harkokin sadarwar Intanet, sai Najeriya ta samu wayoyin sadarwa masu tsawon kilomita dubu 120 domin hada hanyoyin sadarwar Intanet a tsakani manyan sassan kasar nan. Farfesa Umar dambatta, ya bayyana haka ne a Abuja a […]

Najeriya tana bukatar wayoyin masu tsawon kilomita dubu 120 don inganta sadarwar Intanet – Dambatta

Babban Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) Farfesa Umar Garba dambatta ya ce idan ana son cimma nasarar inganta harkokin sadarwar Intanet, sai Najeriya ta samu wayoyin sadarwa masu tsawon kilomita dubu 120 domin hada hanyoyin sadarwar Intanet a tsakani manyan sassan kasar nan.

Farfesa Umar dambatta, ya bayyana haka ne a Abuja a karshen mako, inda ya ce kilomita dubu 38 kadai aka cimma kan hakan a yanzu.

Yana magana ne lokacin da ya karbi bakuncin Majalisar Bayar da Shawarwari kan Tsare-Tsaren Masana’antu da Inganta Gasa a karkashin jagorancin Misis Edirin Akemu.   

Farfesa dambatta ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cea gwamnatocin jihohi 36 na kasar nan suna aiki da matsayar Majalisar Tattalin Arzikin kasa (NEC) game da tsararriyar hanyar cajin kudin wayoyin da ake binnewa daga kamfanonin sadarwa wadda ta ce a rika karbar Naira 145 kan kowace mita ta wayar sadarwar da aka binne a kowane bangare na kasar nan.

“Batun hakkin hanya wani batu ne da aka kasa magancewa duk da akwai wasu takardu da suke jagora ne kan abin da za a iya caza,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Ba za mu tilasta jihohi su caji Naira 145 kan kowace mita ta babbar wayar ba. Amma Gwamnatin Tarayya za ta iya yi, kuma za ta iya ganawa da gwamnoni ta sa su nuna da gaske suke yi, domin tabbatar da an bi ka’idojin na NEC sau da kafa.”

Shugaban Hukumar NCC din ya nemi a kara inganta horarwa kan Ilimin Kimiyyar Labarai da Sadarwa (ICT) a kasar nan domin a samu damar cin cikakken alfanun shirin komawa watsa labarai ta Intanet da ke gudana a duniya.

Ya ce a yayin da Najeriya take kokarin giggina harkokin kimiyyar sadarwa, yunkurin zai iya zama asara “Idan ba a samu rungumar kimiyyar sadarwa tare da aiki da ita ba domin cin gajiyar sauyin da ake samu wajen watsa labarai ta Intanet.”