Najeriya tana goyon bayan kafa kasar Falasdinu
A farkon nan ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana goyan bayansa game da fatan kafa kasar Falasdinu don kawo karshen rikicin da Falasdinawa ke fuskanta a yankin Gabas ta Tsakiya.Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da ya ke ganawa da Sarkin katar Sheikh Tamim bin Hammad al Thani, inda ya ce Najeriya na goyan […]
A farkon nan ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana goyan bayansa game da fatan kafa kasar Falasdinu don kawo karshen rikicin da Falasdinawa ke fuskanta a yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da ya ke ganawa da Sarkin katar Sheikh Tamim bin Hammad al Thani, inda ya ce Najeriya na goyan bayan daukacin kudirorin da Majalisar dinkin Duniya ta amince da su saboda a samu kasashe biyu wato Israila da Faladinu.
Har ila yau, ya shaida wa Sarkin cewa Najeriya za ta hada kai da katar don ganin hakar Falasdinawan ta cimma ruwa.
A bara ne zamanin Shugaba Goodluck Jonathan Najeriya ta ki kada kuri’ar goyan bayanta ga kasar Falasdinun a kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin Duniya.