Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025
Ƙasashen biyu za su yi wasan na sada zumunta gabanin fara gasar AFCON ta 2025.
Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da ƙasar Masar kafin fara gasar Kofin Afrika da za a yi a Maroko.
Wasan zai gudana ne a ranar 11 ga wata. Disamba, da misalin ƙarfe 7 na dare, a filin wasa na Cairo da ke Masar.
- EFCC ta tsare Malami kan binciken kuɗaɗen Abacha
- Real Madrid za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago
Za a yi wasan ne kwana shida kafin a fara gasar da ƙasashe 24 za su fafata a cikinta.
Najeriya za ta fara wasanta na farko a ranar 23 ga watan Disamba da Tanzania.
Ita kuwa Masar za ta buga wasanta na farko da Zimbabwe a ranar 22 ga watan Disamba.
A tarihi, Masar ce tafi lashe Kofin Afrika inda ta lashe gasar sau bakwai, yayin da Najeriya ta lashe sau uku.