Najeriya za ta bunƙasa tattalin arziƙi ta hanyar faɗaɗa masana’antu
An mayar da hankali ne kan buƙatar gaggauta faɗaɗa tattalin arziƙin ƙasar da kuma bunƙasa fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba zuwa ƙasashen waje.
Makomar tattalin arziƙin Najeriya zai rage dogaro a kan man fetur, kamar yadda masana da masu tsara manufofi suka tattauna a taron bankin First City Monument Bank (FCMB), da aka yi a baya-bayan nan.
An mayar da hankali ne kan buƙatar gaggauta faɗaɗa tattalin arziƙin ƙasar da kuma bunƙasa fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba zuwa ƙasashen waje.
- Ambaliya ta kashe mutum 49, ta raba 41,344 da muhalli a Arewa — NEMA
- Jerin masu horas da ’yan wasan Super Eagles a tahiri
Mahalarta taron sun bayyana irin damar da ake da ita a bangaren noma, masana’antu, hakar ma’adanai, da kasuwanci.
Manajan Daraktan FCMB, Yemisi Edun, ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwa domin cimma wannan sabon tsarin.
Ta ce, “Ta hanyar samar da yanayi mai ɗorewa, bunƙasa muhimman kayan more rayuwa, da kuma samun kuɗaɗe masu dorewa, za mu tabbatar da nasara a ɓangaren fitar da kayayyakin Najeriya.”
Edun, ta kuma nuna rawar da bankin ke takawa wajen taimakawa fitar da kayayyaki da kuma aike kuɗaɗe daga waje.
Babban baƙo a wajen taron, Nonye Ayeni, Shugaban Hukumar Kula da Fitar da Kayayyaki ta Najeriya (NEPC), ya jaddada buƙatar masu fitar da kayayyaki su ƙara yawan kayayyakin da suke samarwa da inganta su don yin gogayya a kasuwannin duniya.
Ya ambaci shirin “Export 35 Refined” na hukumar, wanda ya ƙaru da kuɗaɗen shiga ta hanyar tallafa wa kayan noma.
Jami’an gwamnati, ciki har da Adewale Adeniyi, Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam, sun tattauna kan matakan sauƙaƙa kasuwanci, da kuma sauya tsarin Kwastam zuwa na zamani.
Manajan Daraktan Bankin Fitar da Kayayyakin Najeriya (NEXIM), Abubakar Bello, ya tattauna kan ƙoƙarin cike giɓin da ake samu na kuɗaɗe da bunƙasa kasuwanci.
Taron ya gabatar da yadda Najeriya za ta rungumi sabon tsarin tattalin arziƙi mai ƙarfi, tare da bambancin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da kuma samun ci gaba mai ɗorewa ta hanyar amfani da manyan albarkatun ƙasa ta hanyar bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire a ɓangarorin da ba na man fetur ba.