Najeriya za ta fafata da Masar domin neman na uku a gasar AFCON
Cikin wasanni 7 na baya da ƙasashen suka fuskanci juna, Masar ta yi nasara sau 4, yayin da Najeriya ta yi nasara sau biyu.
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Nigeria, Super Eagles, za ta kece raini da ƙasar Masar a wasan neman mataki na uku na gasar Kofin Nahiyyar Afirka da ke gudana a Morocco.
Kasashen za su yi karon-battar ne a da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Asabar, gabanin buga wasan ƙarshe na gasar da za a yi da ƙarfe 8 na dare a ranar Lahadi tsakanin Senegal da Morocco.
- Kano Pillars ta samu nasara karon farko a wasan baƙunta a bana
- Limaman Najeriya sun gudanar da taron addu’a kan matsalar tsaro
Duk a jiya Laraba ce a ƙasashen biyu suka rashin nasara a wasan kusa da na ƙarshe da suka fafata, inda Senegal ta yi ta yi waje rod da Masar, yayin da Morocco ta yi galaba a kan Najeriya bayan wasan da suka fafata ya kai su zuwa bugun fanareti.
Cikin wasanni 7 na baya da ƙasashen suka fuskanci juna, Masar ta yi nasara sau 4, yayin da Najeriya ta yi nasara sau 2, sannna kuma aka yi canjaras sau 1.
A cikin dukkanin wasannin da suka fuskanci juna a baya, Masar ta samu nasarar zura ƙwallaye 10 yayin da Najeriya ta zura ƙwallaye 7 a raga.