Najeriya za ta fara ba wa Chadi wutar lantarki

Gwamnatin Tarayya na shirin fara samar da wutar lantarki ga kasar Chadi daga Najeriya.

Najeriya za ta fara ba wa Chadi wutar lantarki

Gwamnatin Tarayya ta fara shirin samar da wutar lantarki ga kasar Chadi daga Najeriya.

Gwamnatin Chadi ta bukaci a farfado tattaunawar da ke tsakanin kasashen domin Najeriya ta fara ba ta wutar lantarki.

Jakadan Chadi a Najeriya, Abakar Saleh Chahaimi ne ya yi rokon a ziyarsa ga Ministan Wutar Lantarki na Najeriya, Injiniya Abubakar Aliyu a Abuja.

Chahaimi ya ce a baya kasashen sun fara kan yadda Najeriya za ta rika ba wa Chadi wutar lantarki, amma ba a kai ga kulla yarjejeniyar ba.

Don haka ya roki ministan ya taimamaka wajen sake taso da maganar, domin a cewarsa, kasashen biyu za su amfana da hakan.

Jakadan ce yarjejeniyar da Bankin Duniya ya dauki nauyi kan samar da wutar lantarki daga Kamaru zuwa Chadi zai kawo karin hadin kai da cigaba a tsakanin kasashen Afirka.

A nasa bangaren, Ministan Wutar Lantarki, Injiniya Abubakar Aliyu, ya ba da tabbacin ci gaba da maganar samar wa Chadi wutar lantarki daga Najeriya.

A cewarsa daraktocin ma’aikatarsa da ke da masaniyar inda batun ya kwana za su ci gaba da aiki a kan lamarin.

Yin hakan, a cewarsa wani bangare ne na gudunmmawar Najeriya ga ci gaba da hadin kan kasashen Afirka.