Najeriya za ta fara fitar da dawa zuwa kasashen waje – ICRISAT

Aakilin Hukumar Bincike kan Ingancin Amfanin Gona (ICRISAT), Mista Hakeem Ajeigbe ya ce nan bada dadewa ba Najeriya za ta fara fitar da dawa zuwa kasashen waje. Kafar labarai ta Premium Times ta ruwaito Mista Hakeem Ajeigbe yana shaida wa manema labarai haka, inda ya ce, gwamnati ta kammala shiri tsaf domin ganin Najeriya ta […]

Najeriya za ta fara fitar da dawa zuwa kasashen waje – ICRISAT

Wata gonar dawa

Aakilin Hukumar Bincike kan Ingancin Amfanin Gona (ICRISAT), Mista Hakeem Ajeigbe ya ce nan bada dadewa ba Najeriya za ta fara fitar da dawa zuwa kasashen waje.

Kafar labarai ta Premium Times ta ruwaito Mista Hakeem Ajeigbe yana shaida wa manema labarai haka, inda ya ce, gwamnati ta kammala shiri tsaf domin ganin Najeriya ta fara sayar wa kasar Britaniya nikakkiyar dawa.

“Kasar za ta yi amfani da ita  ce wajen sarrafa lemon Maltina da alawar cakulat da biskit da sauran kayan makulashe da na marmari. Mutane da dama sun san cewa ana amfani da dawa wajen yin tuwo da kunu ne kawai sai kuma masu yin  giya da ita. Baya ga wadannan abubuwa akwai abubuwa da dama da ake sarrafawa da dawa,” inji shi.

Ya ce, “A yanzu mun horar da mata a kauyuka kan yadda ake yin guguru da dawa sannan da yin garin dawa domin soya fanke da sauran abinci.”

Mista Ajeigbe ya ce Gwamnatin Tarayya  ta karkata wajen inganta amfani da dawa ne ganin yadda mutane da dama suka daina cin dawa a kasar nan.

“Yanzu manoma sun koma ga noman shinkafa da masara inda hakan ya sa babu abincin da mutum zai ci musamman a Arewa da babu shinkafa ko masara a ciki. Cin irin wannan abinci ne ya sa ake yawan kamuwa da ciwon suga da yawan kiba da sauran cututtuka,” inji shi.

Mista Ajeigbe ya yi kira ga mutane su rika cin kayan abincin da suke inganta karfin garkuwar jiki musamman kayan lambu da ganyayyaki.