Najeriya za ta fara fitar da tataccen mai kasar waje a 2024 —NNPCL

NNPC ya ba wa ’yan Najeriya tabbacin cewa cikin watanni uku masu zuwa ba za a samu karancin mai yadda ake gani ba a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara

Najeriya za ta fara fitar da tataccen mai kasar waje a 2024 —NNPCL

An ƙara farashin man fetur a Najeriya

Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) Mele Kyari ya ce Najeriya za ta zama kasa mai fitar da tataccen man fetur da dangoginsa zuwa kasashen waje a shekarar 2024 mai kamawa.

Mele Kyari ya kuma ba wa ’yan Najeriya tabbacin cewa cikin watanni uku masu zuwa ba za a samu karancin man fetur ba, kamar yadda ake gani a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

“Ina tabbatar wa shugabannin majalisa ba za a fuskanci karancin mai ba.

“Za ku ji ana ta yada labarin layuka a gidajen mai, amma ba gaskiya ba ne,” in ji Mele Kyari.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci shugabannin majalisar dattawa.

Ya kara da cewa NNPC zai gyara matatar mai ta garin Fatakwal a wata mai kamawa, sannnan matatar mai ta Warri ta biyo baya a farkon 2024.

Haka zalika, ya yi hasashen NNPCL zai samu ribar da ta kai triliyan biyu a shekarar 2023 da ke dab da karewa.

Kyari ya shaida wa shugabannin majalisar dattawa cewa amincewa da sabuwar dokar man fetur, ta saka man ya wadata kuma a farashi mai sauki a kasar nan.

Da yake jawabi kan matsalar fasa bututu da satar mai, Kyari ya ce jami’an tsaro na musamman da ke yaki da bata-garin, sun taimaka musu wajen kwato gangunan danyen mai na kusan naira miliyan biyu.

Da yake jawabi, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya gode wa kamfanin man bisa hadin kai da ya bai wa Gwamnatin Tarayya  wajen cire tallafin man fetur.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta