Najeriya za ta fito da sabon shirin dakile barazanar ’yan ta’adda a Arewa maso gabas
Gwamnatin Tarayya tana kan fito da wani shiri na musamman domin wargaza barazanar ta’addancin Boko Haram, wanda a karkashin shirin, mai taken DDRR, zai maida hankali wajen canza tunanin ’yan ta’adda, sasanci da kuma maido su cikin al’umma, da nufin samar da zaman lafiya da kuma nemo tallafin kasashen duniya ga wadanda matsalolin Boko Haram […]
Gwamnatin Tarayya tana kan fito da wani shiri na musamman domin wargaza barazanar ta’addancin Boko Haram, wanda a karkashin shirin, mai taken DDRR, zai maida hankali wajen canza tunanin ’yan ta’adda, sasanci da kuma maido su cikin al’umma, da nufin samar da zaman lafiya da kuma nemo tallafin kasashen duniya ga wadanda matsalolin Boko Haram suka shafa a Arewa maso gabashin Najeriya.
Shugabar kula da shirin dakile ayyukan ta’addanci a ofishin Mai Ba Shugaban kasa Shawara ta Fuskar Tsaro, Uwargida Catherine Udida ce ta bayyana haka a ranar 14 ga Nuwamba. Ta ce wannan sabon shirin zai dora ne a kan irinsa da aka gudanar a watan Oktoba na 2015 da kuma makamancinsa da aka gudanar da Agusta na bana (2017).
Udida ta ce wannan na daya daga cikin kokarin gwamnati na musamman da take yi da nufin dakile ta’addancin kungiyar Boko Haram. Kamar yadda ta ce, domin ganin an samu nasara, ofisoshin Mai Ba Shugaban kasa Shawara ta Fuskar Tsaro da na Ma’aikatar Shari’a da na Ma’aikatar Tsaro, sun shirya taron bita tare da hadin gwiwar kungiyar da ke kula da al’amuran ’yan gudun hijira ta duniya (IOM), domin tattaunawa dangane da wannan shiri.
Ta ce wadannan tsare-tsare za su tallafa wa sauran shirye-shiryen da suke a kasa domin samun nasarar dakile ta’addanci da ’yan ta’adda da amsar wadanda suka tuba da gyara masu halaye domin ci gaba da mu’amala cikin jama’a. Ta ce kuma wannan sabon shiri zai hada har da duba al’amarin da ya shafi shari’a da sauransu.
Ta ce wannan taron bita zai hada da masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da tsaro, wadada suka hada da Mai Ba Shugaban kasa Shawara ta Fuskar Tsaro, Ofishin Ministan Shari’a, Shugaban Hukumar Tsaro, Ma’aikatar Tsaro, Ma’aikatar Cikin Gida, Ma’aikatar Al’amuran Mata da Walwalar Jama’a, Ma’aikatar Al’amuran Kudi Da Tsare-Tsare, Cibiyar Wayar Da Kan Al’umma (NOA), Hukumar ’Yan sanda, Ofishin Hafsan Sojojin kasa da Cibiyar Samar Da Aikin Yi Ta kasa da sauransu.
Ofishin gwamnonin jihohin Borno da Adamawa da Yobe za su halarci taron su ma, a matsayin wakilan mazabunsu da al’ummominsu, domin su tabbatar da cewa ana daukar matakan da suka dace a jihohinsu. Domin karkare shirin, za a gudanar da Babban Taro a ranar 5 ga watan Disamba na bana a Abuja, wanda zai tattara wadannan hukumomi da cibiyoyi da aka ambata a baya da kuma gwamnonin da wadannan al’amura na ta’addanci ke shafar jihohinsu na Arewa maso gabas, kamar Borno, Adamawa da Yobe.