Najeriya za ta fuskanci tsadar abinci a 2022 — NBS

Binciken ya bayyana yadda kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi.

Najeriya za ta fuskanci tsadar abinci a 2022 — NBS

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce akwai yiwuwar samun karanci tare da tsadar kayan abinci a Najeriya a 2022.

Wannan na kunshe ne a cikin wani bincike da hukumar ta fitar, inda ta ce za a fuskanci tsananin tsadar a Najeriya saboda karancin noma a wasu yankuna.

Mutane da dama dai na kokawa kan yadda kayan abinci kamar su shinkafa, wake da man gyada suka yi tashin gwauron zabi.

Samun karancin ruwan damuna a wasu sassan Najeriya, shi ma na iya zama babbar barazana na karancin abincin, kamar yadda NBS ta bayyana.

Kazalika, rahoton na NBS ya ce farashin kwai ya karu a wasu wuraren da kusan kashi 25 cikin 100.

Har wa yau, a wasu kasuwannin ana sayar da kilon tumatur akan N342, a maimakon Naira 286 a watan Satumba.

NBS ta sake bayyana cewar, an samu karin kudin ababen sufuri da suka hada da mota, jiragen sama da na kasa a fadin Najeriya.

Haka kuma wani bincike da kamfanin United Capital Management ya yi, ya gano cewa hauhawar farashin kayan abinci da aka samu daga watan Satumba zuwa Oktoba, wata alama ce da ke nuni da irin halin da kasar ke ciki.