Najeriya za ta hadu da Nijar a wasan sada zumunta

Ana sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kece raini da Nijar a wasan sada zumunta da zai gudana a ranar 8 ga watan gobe. Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ce ta sanar da labarin a kafar sadarwarta. Hukumar ta ce ana sa ran za a yi wasan ne a […]

Najeriya za ta hadu da Nijar a wasan sada zumunta
Najeriya za ta hadu da Nijar a wasan sada zumunta

Ana sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kece raini da Nijar a wasan sada zumunta da zai gudana a ranar 8 ga watan gobe.

Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ce ta sanar da labarin a kafar sadarwarta. Hukumar ta ce ana sa ran za a yi wasan ne a filin kwallo na garin Fatakwal. Hukumar ta ce tuni ta fara tuntubar gwamnatin Jihar Ribas a kan yadda wasan zai kasance sai dai akwai yiwuwar a mayar da wasan zuwa wani wuri idan filin kwallon Fatakwal din bai samu ba.
Tuni kasar Nijar ta tabbatar da cewa za ta halarci wasan da Najeriya ta shirya a wata takardar amincewa da ta aika wa hukumar NFF ta hannun Jakadanta da ke Najeriya.
Wannan wasa da Najeriya ta shirya, tamkar gwaji ne ga wasan share fage na hayewa gasar cin kofin Afirka da zai gudana a tsakanin Najeriya da Tanzaniya a watan gobe. Wasan Najeriya da Tanzaniya zai kasance wasan farko ga sabon kocin Super Eagles Sunday Oliseh.

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja