Najeriya za ta iya ciyar da kasashen Afirka da dama – Mannir Dan Ali

Babban Edita kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin Jaridun Daily Trust da Aminiya, Malam Mannir Dan Ali, ya ce ba za a iya cimma burin da ake da shi ba na sauya akalar noma daga na dauri wajen samun abinci kawai zuwa na kasuwanci ba  sai dukkan masu ruwa-da-tsaki a harkar sun dauki matakan da […]

Najeriya za ta iya ciyar da kasashen Afirka da dama – Mannir Dan Ali

Babban Edita kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin Jaridun Daily Trust da Aminiya, Malam Mannir Dan Ali, ya ce ba za a iya cimma burin da ake da shi ba na sauya akalar noma daga na dauri wajen samun abinci kawai zuwa na kasuwanci ba  sai dukkan masu ruwa-da-tsaki a harkar sun dauki matakan da suka kamata.

Malam Mannir Dan Ali ya fadi haka ne a Legas a ranar Talata, yayin bude Taron Noma da Baje Koli Karo na Uku da Jaridar Daily Trust ta shirya; inda ya ce gwamnatoci a dukkan matakai da cibiyoyin hada-hadar kudi da kamfanonin da hukumomin da suka shafi harkar noma da manoman kansu da sauran masu hannu a harkar suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen tafiyar da harkar noma da kiwo a kasar nan.

Ya ce akwai bukatar gwamnatoci da cibiyoyin kudi su kara azama ta fuskar samar da kudaden tallafi ga harkar noma da zimmar kawo gagarumin sauyi don cimma muradun da ake so a bangaren.

A cewar Mannir Dan Ali, “Mun ga yadda gwamnati ta bullo da shirye-shirye daban-daban, kamar a wannan gwamnatin, Shirin nan na Anchor Borrowers a karkashin Babban Bankin Najeriya (CBN), yana da alfanu sosai. Sai dai a bayyane yake cewa, har yanzu akwai bukatar gwamnati ta kara matsa kaimi sosai ta wasu fuskokin da suka shafi noman kai-tsaye.”

Malam Mannir Dan Ali ya ce Najeriya ba wai tana da karfin da za ta iya ciyar da kanta kawai ba ne;  har ma tana da karfin wadata dukkan kasashen da take makwabtaka da ita a yankin yammacin Afirka; amma abin takaicin shi ne ita ma tana dogaro ne da shigo da mafi yawan abincinta daga ketare.

“Ga wadansu daga cikinmu, wadanda ko dai manoma ne ko kuma kwararru a harkar, muna sane cewa har yanzu ana gudanar da noma irin na dauri a Najeriya – duk  da cewa kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na al’ummar kasar sun dogara ne da noma domin gudanar da rayuwar yau da kullum,” inji shi.