Najeriya za ta iya dogara da kasuwancin gwal -Lawalli

Lawalli kauran Namoda mai sarrafa danyen gwal zuwa sarka ne. Aminiya ta tattauna da shi inda ya koka kan yadda ake fitar da danyen gwal waje don a sarrafa shi, ya ce Najeriya za ta iya dogara da kanta ta hanyar kasuwancin gwal. Yaya ka fara harkar sayar da gwal? Sunana Lawalli kauran Namoda, ni […]

Najeriya za ta iya dogara da kasuwancin gwal -Lawalli

Lawalli kauran Namoda mai sarrafa danyen gwal zuwa sarka ne. Aminiya ta tattauna da shi inda ya koka kan yadda ake fitar da danyen gwal waje don a sarrafa shi, ya ce Najeriya za ta iya dogara da kanta ta hanyar kasuwancin gwal.

Yaya ka fara harkar sayar da gwal?

Sunana Lawalli kauran Namoda, ni mutumin Zamfara ne. Na fara sayar da gwal da azurfa da sauransu bayan na koya a wurin Abdullahi Fada a 1996 a kasuwar kofar Mata da ke birnin Kano. Daga nan na dawo Kaduna a shekarar 2001 na bude shagona.
Yaya ake karkasa gwal?
Ana yin haka ne ta darajar tacewar da aka yi masa. Karat 21 da 22 da 23 ko kuma 24. Karat na 24 shi ne ya fi daraja. In aka tace gwal mai nauyin giram 100 sai ya koma giram 90. Wanda ya fi karancin nauyi shi ne mai 6 da 9 da kuma 14, sannan kuma 0.9 shi ne karshe, amma ba shi da daraja a nan. Turawa sun fi amfani da shi. Ana sayar da shi daidai da Naira 6,300 sarka guda.
Sannan Karat 21 ko 22 na kaiwa Naira dubu 15.
Gwal din Dubai ya fi tsada don yakan kai Naira 7,500.
Karat 22 da 24 wanda Larabawa suka fi amfani da shi da kuma masu kudi a Najeriya yakan kai Naira 15, 000 giram guda ke nan. Idan ka yi lissafinsa sau 30 yakan kai Naira dubu 300 sarka guda.
A ina babbar kasuwar gwal ta duniya take?
Tana kasar Indiya, domin sukan haka, sannan su sarrafa, sai kasar Italiya wadda ke sarrafa gwal din Ingila. Amma a yanzu babbar kasuwar gwal a duniya tana kasar Dubai ne.
Yaya ake gane ingancin gwal?
Muna sa wani ruwan sinadari ne, sannan mu goga a dutsen tiles, wanda ake yin gini da shi don gane ko mai kyau ne ko jabu.
Azurfa kuma fa?
Yawancin ’yan Najeriya na son sayen azurfa mai arha ko jabu, wadda take saurin kodewa, sannan ba ta da daraja idan ana so a sayar da ita. Amma mai kyau ba ta kodewa. Masu zafin jiki azurfarsu na komawa baka ko da mai inganci ce. Farashin azurfa ya fara ne daga Naira dubu daya. Ba a cika sayen azurfa ba kamar yadda ake sayen gwal.
Me ya sa ba za mu sarrafa gwal ba?
Gwamnati ba ta son talaka ya samu aikin yi ne. Don hakowa da sarrafa gwal zai samar wa kasar nan da kudaden shiga. Don kasar Saudiyya da Dubai da sauransu sun karfafa hanyar kudin shiga daga man fetur, kasancewar duk inda ka je a duniya, akwai ’yan Najeriya da suke aikin likita da sauransu, amma shugabanni sun fi son kashe kudin shigar da ake samu daga man fetur, shi ya sa idan aka samu faduwar farashin man fetur muke shan wuya.
Ina kuke zuwa sayen gwal?
Ina zuwa Dubai ne don sayo gwal don mu samu na sawa a bakin-salati. Su ’yan Dubai suna zuwa kasar Indiya ne su sayo da yawa, sannan su sayar. Najeriya na iya dogaro dungurungun ga harkar gwal. Don mutane da yawa za su zo kasar nan don sayen gwal. Duk dan Najeriya da ya shiga harkar gwal a Indiya zai shiga uku in an kama shi.
Ko kana sayen danyen gwal ka sayar a kasashen waje?
Eh, da na fara sayowa daga Nijar da Mali ina kai wa Dubai, amma na bari.
Me ya sa mata ne suka fi sayen gwal?
Dalilan sun hada da yin kwalliya don nuna isa, don sayarwa idan sun bukaci kudi.
Ko kuna yin amfani da risidi?
Eh, sai dai mafi yawan matan Kaduna ba sa iya ajiye risidi. In sun zo sayarwa, in ka ce musu ina risidi, sai su ce ba su san inda yake ba. Amma sun san inda gwal yake. Amma mafi yawan matan Kano suna kula da risidinsu.
Yaya kuke da barayin gwal?
Muna lura da wanda ya zo sayar da gwal, muna lura da ko ya isa ya mallaki gwal din. Don maganin fadawa cikin rigima. Za mu nemi risidi, in babu ba ma saye. Muna kuma tambayar nawa mutum yake nema ya sayar ko nawa ya saya. In mutum ya kawo gwal din dubu 200, ya ce yana son Naira dubu 20 sai mu ce ba za mu saya ba.
Yaya kasuwar gwal take a yanzu?
A zamanin Obasanjo da ’Yar’aduwa muka caba, a yanzu sai dai mu fito mu yi hira mu koma gida.
Da gaske ne mata na zama a shagon sayar da gwal a yi awowi ana ciniki?
Eh, kasan mata suna da ja a ciniki, sannan su sanya sarkar a wuya su gwada a madubi su sauya wani har dai a dace. Hakuri muke a ciniki da mata. Mata ne abokan cinikinmu ba maza ba. Sai dai wadanda suka rako matansu.
Ko ka taba shiga rigimar kasuwancin gwal?
Na taba a bakin Asibitin Gwauron Dutse a Kano, a lokacin ina koyan harkar a wurin Alhaji Tukur and Hassan Seti. Lokacin ana sayar gwal giram daya a kan na Naira 600. An kulle ni a ofishin ’yan sanda na Gwauron Dutse lokacin DPO Bala Gwauron Dutse.
In kun sayo gwal, kuna barin jakarku a wurin masu lodin jiragen sama, ko ratayawa kuke?
Gwal na da daraja a ko’ina a duniya. Duk mai safararsa yana rike da jakarsa a hannunsa, idan ba haka ba ya sha mamaki.