Najeriya za ta iya dogara da noma

Edita ka bani dama yin tsokaci kan harkar noma a Najeriya. Hakika Allah ya albarkaci Najeriya da kasar noma mai albarka wacce kusan duk abin da muke da bukata za a iya noma shi a Najeriya. Ga kuma tafkuna da madatsun ruwa (Dams) da Allah ya albarkace mu da su, wadaanda koda rani za mu […]

Najeriya za ta iya dogara da noma
Najeriya za ta iya dogara da noma

Edita ka bani dama yin tsokaci kan harkar noma a Najeriya. Hakika Allah ya albarkaci Najeriya da kasar noma mai albarka wacce kusan duk abin da muke da bukata za a iya noma shi a Najeriya. Ga kuma tafkuna da madatsun ruwa (Dams) da Allah ya albarkace mu da su, wadaanda koda rani za mu iya noma da su. Abin takaici wadannan albarkatu, sai an shigo da kayan abinci daga kasashen waje. Kasancewar gwamnati ba ta taimakon manoma da iri mai inganci da  magungunan kashe kwari da taki da injinan zamani na noma. Gwamnatocin baya kafin gano man fetur sun tallafa wa harkar noma, amma na yanzu sun yi watsi da harkokin noma gaba daya. A baya mun ga ci gaba na harkar noma irin su Dalar gyada a Kano da Cocoa a garuruwan Ibadan da Jihar Osun da auduga a Katsina da fatu da kiraga da manyan abubuwa masu kawo wa Najeriya kudin shiga. Samun man fetur yasa aka yi watsi da su. Ina kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi da ta kananan hukumomi da su tallafa wa harkar noma da manoma da kiwo da duk abubuwan da suke bukata, domin rage dogaro da man fetur da kuma samar wa matasa aikin yi.

Addu’a ga kasa
Allah ka ba mu zaman lafiya a Arewa da kasa baki daya sako daga, Shamsiddeen Rabe Daura [email protected].

A yi adalci shugabanni
Salam Edita ina so ka ba ni dama in yi kira ga shugabanin Najeriya da cewa ya kamata su yi wa al’umma mulkin gaskiya da adalci, saboda a fili take matsalar Najeriya ta samo a sali ne daga rashin adalci a tsakanin al’umma. Ina fatan shugabanin za su yi amfani da wanan kira nawa  Daga Umar Idirisa Askira, Jihar Borno 07034478412.

Ga gwamna dakingari
Asslam. Jaridar Aminiya dan allah ku isarmin da sakona kasancewar shine na farko zuwa ga gwamnatin jahar kebbi wadda ke kula da shimfida tituna cewa ina aka kwana kan gina titi a cikin garin maiyama wanda a tuni an kammala awon, amma ga shi mun ji tsit ko sai zabe ya karato sannan a fara yi mana gafara.. Don da wannan nake kira ga Gwamnatin dakingari cewa, muna nan karamar Hukumar Maiyama, babu wani romo da muka dandana a cikin mulkinsa. Daga karshe ina kira ga ’yan uwana matasa cewa mun ga yadda shekaru hudu suka kaya, babu wata moriya da aka yi mana. Don haka mun shirya tsaf don tumbuke duk wani azzalumin shugaba da yardar Allah. Daga Nasiru Musa Maiyama, Jihar Kebbi 08062206733/08084151555.

Ko ’yan Chibok ne?
Edita  A kwanakin nan ‘yan mata sun kai hare-haren kunar bakin wake sau hudu a Kano. Mahukuntan Najeriya sun ce an cafke wata yarinya da ta nemi kai hari daure da bom a jikinta. Wannan al’amari ya sa ‘yan Najeriya cikin fargaba, saboda yadda aka fara samun ‘yan mata suna kai hari bayan sace ‘yan matan garin Chibok sama da 200 a Jihar Borno. “Allah ya sa ba ‘yan matan Chibok ba ne ake amfani da su wajen kai harin kunar bakin wake a Kano.” Daga Anas Saminu Ja’en Makera,Kano 07033882307,08188742103.

Ga Gwamnatin Katsina
Assalam Aminiya ina so a mika min kirana ga gwamnatin Jihar Katsina akan ta gaggauta daukar matakin dakile yaduwar cutar kwalara da ta kunno kai a wasu sassan yankin Funtuwa da kewaye. Domin kuwa yanzu haka majinyata suna nan birjit babu gado a asibitoci sai dai a kwantar da masu majinya a kasa, kuma a waje akan tabarma, don baki daya asibitocin sun cunkushe. Da fatan gwamnati za ta kara zage damtse wajen yakar wannan cuta. Ina addu’ar Allah ya kawo mana dauki, Ya yaye mana wannan bala’i amin.
Daga Isah Abdussalamu Funtua Shugaban Shafin Muryar Matasan Najeriya. [email protected]

Haba talakawa!
Edita don Allah ka ba ni dama in yi tsokaci kan abinkunyar damu talakawa keyi musamman idan akace gawani mai rike da mukamin gwamnati ya yi wata tafiya, ya dawo sai ka ga talakawa sun yi gangami wajen taryar shi, Hakika yin haka akwai takaici, kodayake hakan yana da alaka da talauci, saboda da dama ana raba wa masu zuwa tarar ne kudi, kuma kudin ba za su magance mana talauci ba. To, ni ina ganin irin wannan gangamin da talakawan ke yi yana nuna wa duniya cewar masu jagorantarmu suna gamsar da mu, kuma kowa yasan da dama daga cikin masu mulkin mu ba sa kaunarmu, suna kaunar kawunansu ne da iyalansu. Don haka nake bai wa ‘yan uwana talakawa shawara ya kamata mu kauracewa duk wanda ya je ya gama sharholiyarsa, tare da barnatar da dukiyarmu wajen taroshi. Daga Aminu Abdu Baka noma, Sani Mainagge, Jami’in Hulda da Jama’a (PRO) na kungiyar Muryar Talaka reshan Kano 08099479880.

Ga makiyan Jihar Adamawa
Salam Editan Aminiya Hausa,  Tabbas Jihar Adamawa ba ta da makiya a duk duniyan nan irin jam’iyan PDP dama yan Majalisan dokokin jihar domun abun bakin ciki ne da takaici a irin Mummunan yanayi na Rashin tsaro dama yawaitan Kai hare hare da tashim bam dama Dokan Tabaci dake faruwa a Jihar Adamawa. Wai har dan Majalisa zai amince wasu daga Abuja su bashi kudi domin ya saka jiharsa cikin matsala, ta hanyar cire Gwamna Murtala Nyako. Kowa yasan da cewa irin wadannan matakai ana daukar su ne kawai domin ruguza Arewa, musamman ma a zaben 2015, Mu ’yan Arewa, don haka wallahi idan ba mu daina munafintar junan mu akan kudi ba, to wallahi wahala ma ba mu ga komai ba. Allah ka hada kan Arewa da ’yan Arewa. Daga Amadu Manager Bauchi Unguwar Karofin Madaki. 08065189242.

Ga FDk
Salam Edita, don Allah Ka mikan gaisuwa ta bangirma ga Editan FDk, don naji kwana biyu shiru. Allah Yasa dai lafiya. Daga Haruna Uba 08093589601.

A sasanta rikicin Najeriya
Editan Aminiya ina so ka ba ni dama in yi tsokaci kan tashin hankalin d ayake addabar kasata Najeriya, musamman Arewa maso Gabas; Barno Yobe da Adamawa. Ina kira a sasanta tsakanin Gwamnatin Tarayya da maharani. Domin muna cikin tashin hankalin kisan rayuka da yawan ’yan gudun hijira. Allah Ya kawo mana mafita. Amin. Daga kasaimu Aliyu Sardaunan Matasan Asada, Jihar Sakkwato 08034376194.

Ga ’yan Najeriya
Edita ka mika sakona ga ’yan Najeriya, wai shin sau nawa muke aikata abin dab a daidai ba? Lallai ya kamata mu gyara. Idan muka daina aikata mummuna, muka rika yin kyawawan ayyuka, sai mu dage da addu’a, Allah Zai sama mana mafita. Domin Shi Allah Mai Rahama ne, kuma ghafurrur Rahim ne. Allah Ya zauanr da kasarmu Najeriya lafiya. Amin. Daga Ummi T/Wada Kd 07068743172.

A daina gotn bayan zalunci
Salam. Duk mutumin da zai goyi bayan gwamnatin da ba ta kula da bai wa al’umma kariyar rayuka da dukiyoyinsu, to da kyar in ba sai ya fi ’yan Boko Haram zalunci ba. Allah Ya yi mana kyakkyawar makoma. Daga Isyaku Zariya 08031575851.

Maganin sauro
Don Allah ku isar da sakona ga kamfanin Moskuito coil maganin sauro na wayar leko, wanda ake sayarwa Naira 15. Domin yana cutar da talaka. Lallai a yi gyaran duk d aya dace; ko a sanar da al’ummar hanyar amfnai da shi mafi dacewa. Dafan in kunne ya ji, to jiki ya tsira. Daga Sani Ya-Malam Kano 08126466663.