Najeriya za ta iya fadawa cikin matsin tattalin arziki- Gwamnan CBN

Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana fargabarsa akan cewa, Najeriya za ta iya fadawa cikin matsin tattalin arziki idan ba a dauki matakan magance yawan rashin ayyukan yi ba a Najeriya da wasu matsaloli da ake fuskanta a fannin tattalin arziki. Gwamnan CBN Godwin Emefiele, ya bayyana hakan ne a yau yayin […]

Najeriya za ta iya fadawa cikin matsin tattalin arziki- Gwamnan CBN

Godwin Emefiele, Gwamnan Babban Bakin Najeriya (CBN).

Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana fargabarsa akan cewa, Najeriya za ta iya fadawa cikin matsin tattalin arziki idan ba a dauki matakan magance yawan rashin ayyukan yi ba a Najeriya da wasu matsaloli da ake fuskanta a fannin tattalin arziki.

Gwamnan CBN Godwin Emefiele, ya bayyana hakan ne a yau yayin gabatar da jawabi a mai taken ‘matsalolin da suka dabaibaye harkar kudade a duniya’ wanda aka yi a jami’ar Benin.