Najeriya za ta iya lashe kofin duniya idan…. George Weah
Shugaban kasar Laberiya, George Weah ya ce kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles za ta iya lashe kofin kwallon kafa na duniya da za a yi a Rasha daga watan Yunin bana idan ta yi kyakyawan shiri. George Weah ya fadi wannan kalami ne a lokacin da ya kawo wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyarar […]

Shugaban kasar Laberiya, George Weah ya ce kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles za ta iya lashe kofin kwallon kafa na duniya da za a yi a Rasha daga watan Yunin bana idan ta yi kyakyawan shiri.
George Weah ya fadi wannan kalami ne a lokacin da ya kawo wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyarar wuni daya a ranar Litinin da ta gabata a Abuja.
Ya ce “Idan Najeriya ta yi kyakkyawan shiri ta hanyar biya wa ’yan kwallonta kudadensu a kan lokaci, sannan ta yi kyakkyawan shiri a kan lokaci sannan ta ba ’yan kwallon hadin kai da goyon baya ko shakka babu za ta iya lashe gasar cin Kofin Duniya a bana.”
“Burin kowane Shugaba ne ya ga kasarsa ce ta lashe Kofin Duniya don haka Najeriya tana daya daga cikin kasashen Afirka da ake ji da su a bangaren wasan kwallon kafa,” inji Shugaba Weah.
George Weah shi ne bakin fata daya tilo a tarihi da ya taba lashe kyautar Gwarzon dan kwallon kafa na Duniya (Ballon d’ Bor) a shekarar 2005, kuma ya kasance shi ne dan kwallon kafa na farko a duk fadin duniya da ya zama Shugaban wata kasa.
Ya kawo ziyarar Najeriya ce domin ya nemi taimako daga Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen tallafawa kasarsa ta farfado da tattalin arzikinta a bangarori da dama ciki har da bangaren ilimi.