Najeriya za ta samu miliyan 550 don sayo tauraron dan’adam
Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu ya ce bankin kasar China ya amince ya baiwa Najeriya Dala miliyan 550 don ta sayo sabbin tauraron dan’ adam biyu. Ministan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaran fadar shugaban kasa jim kadan bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari. Shittu ya ce bankin China ya […]

Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu ya ce bankin kasar China ya amince ya baiwa Najeriya Dala miliyan 550 don ta sayo sabbin tauraron dan’ adam biyu.
Ministan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaran fadar shugaban kasa jim kadan bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari.
Shittu ya ce bankin China ya amince da biyan kudin bayan gwamnatin tarayya ta kasa biyan kashi 15 cikin dari na tallafin kudin.