Najeriya za ta sayo kayan gwajin COVID-19 na biliyan takwas

Gwamntin Tarayya za ta kashe Naira biliyan 8.4 domin sayen kayan gwajin cutar COVID-19 domin yakar cutar a Najeriya. Majalisar Zartarwa ta kasa ta ce za a saye adadi daban-daban na aun’ika 12 na kayan gwajin ne domin kara karfin hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa wajen yakar COVID-19. Ministan Lafiya Osagie Ehanire, […]

Najeriya za ta sayo kayan gwajin COVID-19 na biliyan takwas

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire

Gwamntin Tarayya za ta kashe Naira biliyan 8.4 domin sayen kayan gwajin cutar COVID-19 domin yakar cutar a Najeriya.

Majalisar Zartarwa ta kasa ta ce za a saye adadi daban-daban na aun’ika 12 na kayan gwajin ne domin kara karfin hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa wajen yakar COVID-19.

Ministan Lafiya Osagie Ehanire, ya bayyana haka bayan zaman Majalisar na ranar Laraba a Fadar Shugaba Kasa, wanda Shugaba Buhari ya jagoranta.

Ehanire ya ce zuwa yanzu cutar ta yadu a Kananan Hukumomi 586, yayin da gwamnati ke kokarin ganin ta magance ta a dukkanin kananan hukumomi 774 da ke fadin kasa.

A ranar Laraba, Gwamnatin Tarayya ta samu gudunmuwar na’urorin taya nunfashi guda 20 daga Gwamnatin Amurka, a yunkurin da ake yi na ganin bayan cutar.

Zuwa yanzu Najeriya a matakan jihohi da tarayya ta sassauta yawancin dokokin da cutar ta coronavirus ta tilasta sanyawa, bayan samun karuwar wadanda suka warke da kuma raguwar masu harbuwa.

A baya-bayan nan an bude makarantu ga dalibai da za su fara jarabawar kammala karatun sakandare, bayan tun da farko gwamnati ta janye dokar hana tafiye-tafiye tsakanin jihohi.

Tashoshin jiragen kasa da na jiragen sama na cikin gida sun koma aiki yayin da ake ci gaba da bude kasuwanni da wuraren ibada.

Bullar cutar coronavirus a Najeriya a watan Fabrairu ya tilasta sanya dokokin hana zirga-zirga da tarukan jama’a tare da daukar matakan kariya.

Dubban mutane sun kamu da cutar, wadanda yawancinsu ke warkewa, duk da cewa ta yi ajalin wasu.