Najeriya za ta tura jirage marasa matuka a kan iyakokinta

Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ta ce nan gaba za ta fara amfani da jirage masara matuka wajen a kan iyakokin kasar

Najeriya za ta tura jirage marasa matuka a kan iyakokinta

Kwamturola-Janar ta Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, Caroline Wura-Ola Adepoju. (Hoto: Twitter/@nigimmigration)

Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta ce za ta fara amfani da jirage masara matuka wajen yin sintiri a kan iyakokin kasar.

Kwamturola-Janar ta hukumar, Caroline Wura-Ola Adepoju, ta ce tuni Gwamnatin Tarayya ta fara tattauna da kamfanin samar da na’uori na Huawei da ke kasar China kan samar da fasahar na’ura wajen sintiri a kan iyakokin Najeriya.

Ta sanar da haka ne a taron Ranar ’Yan Gudun Hijira ta Duniya a ranar Talata.

Game da fargabar ’yan Najeriya kan yiwuwar harin kuskure irin wanda jirgin soja mara matuki ya kai wa masu taron Mauludi a Kaduna, shugabar hukumar ta ba da tababcin cewa babu wata matsala da za a samu wajen amfani da jirage marasa matuka a kan iyakokin kasar.

Ta bayyana cewa za a yi amfani da jirage marasa matuka a kan iyakokin kasar ne kawai wajen tattara bayanai kai-tsaye.